Rikicin da ya tirniƙe jam’iyyar PDP bayan zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni, ya ɗauki sabon salo, yayin da shugabannin ita jam’iyyar a mazaɓar ƙauyen Igyorov cikin Ƙaramar Hukumar Gboko, su ka bada sanarwar dakatar da Iyorchia Ayu Shugaban PDP na Ƙasa baki ɗaya.
An dakatar da Ayu ne a ranar Lahadi, kamar yadda Sakataren Jam’iyya na ƙauyen su Ayu, mai suna Vangeryina Dooyum ya bayyana a madadin shugaban PDP na mazaɓar mai suna Kashi Philip.
Sanarwar ta ce sun dakatar da Ayu ne saboda sun kama shi ya na yi wa PDP zagon ƙasa, wato ‘anti-party’ a zaɓukan da aka gudanar a faɗin ƙasar nan.
“Mun lura a cikin baƙin ciki da damuwa cewa Iyorchia Ayu wanda shi ne Shugaban PDP na Ƙasa, ya kawo wa nasarorin da PDP ta kamata ta samu cikas a zaɓukan da su ka gabata a wanan mazaɓa ta Igyorov,” haka Dooyum ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar.
Sun zargi Ayu wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne da rashin taɓuka komai a zaɓen gwamna da PDP ta yi a jihar Benuwai.
“Bincike ya kuma gano cewa Ayu bai zo Benuwai ya yi zaɓen gwamna da na majalisar jihohi a ranar 18 Ga Maris, 2023 ba.”
PDP ta rasa kujerar gwamnan Benuwai, ta rasa sanatoci biyu da ta ke da su, kuma ‘yan majalisar tarayya 11 da ta ke da su. Dama ‘yan majalisa 12 na tarayya Benuwai ke da su. Yanzu da Gwamna da su ɗin duk APC ta lashe a jihar.
Dooyum ya ce binciken su kuma ya gano cewa yawancin makusantan Ayu duk APC su ka zaɓa, ba PDP ba, shi ya sa PDP ba ta taɓuka komai ba a mazaɓar da aka haifi Ayu.
“A kan haka mun a yanzu ba mu da yaƙini a kan cancantar iya shugabancin jam’iyya a hannun Ayu. Saboda haka mun dakatar da shi a matsayin mamba na PDP. Dakatarwar ta fara tun daga 24 Ga Maris, 2023.”
Primium Times ta tuntuɓi Sakataren PDP na Jihar Benuwai, Bemgba Iortyom, wanda ya ce ba shi da labarin dakatarwar sai a bakin wakilin mu.
Sai dai kuma ya ce shugabannin mazaɓa ne ke da ikon dakatar wa Mamba.
Tsakanin Ayu Da Ortom Gwamnan Benuwai
Tun bayan zaɓen Iyorchia Ayu ya sha fama da Gwamna Samuel Ortom na asalin jihar haihuwar Ayu.
Ortom na cikin gwamnoni biyar masu neman Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu, tunda PDP ta tsaida Atiku Abubakar ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Wannan rikicin ne ya sa gwamnonin biyar, Samuel Ortom, Nyesom Wike na Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Okezie Ikpeazu na Abiya da Seyi Makinde na Oyo ba su goyi bayan takarar Atiku Abubakar ba.
Idan za a iya tunawa, shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya bayyana yadda Ayu ya harzuƙa shi, har shi da mutanen sa su ka fice daga PDP, su ka koma ANPP.