Ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen da aka kammala a Najeriya na LP, Peter Obi ya ce lallai shine ya lashe zaɓen shugaban kasa da aka yi ranar Asabar.
” Ba zan yarda a yi min fashi da rana tsaka ba. Ni ne na lashe zaɓen, kuma kowa ya sani amma aka yi mini murɗiya da karfin tsiya. To ba zan yarda ba.
Obi ya ce zai garzaya kotu, kuma zai kwato kujerar sa da aka kwace masa.
” Yaya za a ce wai ba nine na yi nasara a zaɓen shugaban kasa ba bayan nine na lashe.
Daga nan sai ya yi kira ga magoya bayan sa su yi hakuri su zauna lafiya sannan su kara shirin tunkarar zaɓen gwamna da na ƴan majalisu dake tafe.
” Ina horon ku kakkaɓe katinan ku na zaɓe ku fita ku je ku zaɓi jam’iyyar Labour.
A karshe ya ce dole a mika masa nasarar da yayi, domin ba zai hakaura.
” Da rana tsaka waɗanda ake kira shugabanni suka yi mana murɗiya, suka kwace mana nasarar da muka samu kamar yadda dama can suka tsara. Mun sani ba gaskiya bace kuma muna nan dai za mu ƙalubalanci sakamakon zaɓen daga farko har karshe.
Shima Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon ba. Ya yi kira ga Hukumar zabe ta soke zaɓen a sake shi kaf ɗin shi.
Discussion about this post