Hukumar yaki da Sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama tubabben dan Boko Haram Alayi Madu da wani basarake Baale Akinola Adebayo da muggan kwayoyi.
Kakakin hukunar Femi Babafemi ya sanar da haka a Abuja a farkon wannan mako.
Babafemi ya ce ranar 10 ga Maris jami’an hukumar sun kama gonakin wiwi guda uku a dajin Kajola dake kauyen Kajola a tsakanin jihohin Edo da Ondo.
Gonar wiwin da hukumar ta kama ya kai fadin hekta 39.801546 sannan gonar na sarkin Kajola Akinola Adebayo ne mai shekara 35.
“Hukumar ta kama Adebayo da misalin karfe 2:30 na dare a cikin gonar tare da wasu ma’aikatansa biyu Arikuyeri Abdulrahman mai 23 da Habibu Ologun mai shekara 25.
Babafemi ya Kuma ce hukumar ta kama wani tubabben ɗan Boko Haram Alayi Madu mai shekara 26 a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 9 ga Maris.
Ya ce rundunar ta kama Alayi wanda ya tsinduma Boko Haram tun yana ɗan shekara 9 kuma an kama shi da kilo 10 na ganyen Skunk.
“Alayi ya ce ya siyo ganyen Skunk a Ibadan jihar Oyo a inda aka kama shi a hanyar zuwa kai ganyen jihar Borno.
“Ya shiga harkar siyar da muggan kwayoyi bayan ya tuba daga Boko Haram a shekarar 2021 da bayan haka ne ya koma zama gari Ibadan yana aikin achaba. A wannan harka ne ya fara safarar muggan kway yana kaisu Barno ya na siyar wa.