Jam’iyyar NNPP wacce a itace Rabiu Kwankwaso yayi takarar shugaban kasa da a ka kammala a Najeriya ta bi sahun jam’iyyar PDP ,LP da wasu Jam’iyyun dake kira da a soke zaɓen shugaban kasa da aka yi a kasar nan a karshen makon jiya.
Shugaban jam’iyyar NNPP Rufai Alkali ya ce zaɓen cike yake da kurakuran da su misaltuwa da adalilin haka jam’iyyar sa ta NNPP ke kira da a soke zaɓen kwatakwata a sake sabuwa.
” Baya ga siyan ƙuri’u da aka rika yi, an yi arin gizon su a wurare da dama, sannan kuma dagangar aka ruka kin amfani da na’urar BVAS domin a kwarara wa wasu kuri’un boge don su ci zaɓe.
” A dalilin haka ne muma a jam’iyyar mu mu ke korafi sannan muke kira da a gaggauta soke zaɓen a sake sabiwa fil.
Tun a lokacin da ake bayyana sakamakon zaɓen, jam’iyyar PDP ta nuna ɓacin ranta da kin yarda da sakamakon da ake bayyanawa.
Dino Melaye na PDP ya nemi a dakatar da bayyana sakamakon zaɓen cewa basu gamsu da sakamakon ba.
Jam’iyyar NNPP ce ta zo na huɗu a zaɓen shugaban kasa da kuri’u miliyan 1 da yankai wanda yanwan su a jihar Kano ya ciwo su.