Gwamna Aminu Masari na Katsina ya bayyana wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya na da yaƙinin cewa APC ce za ta yi za ta yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Katsina.
Masari ya shaida wa manema labarai cewa ya gana da Shugaba Buhari ne inda ya shaida masa irin gagarimin shirin cin zaɓen da APC ta yi na gwamna, inda ya yi masa alwashin cewa Dikko Raɗɗa na APC ne zai yi nasara a ranar 11 Ga Maris.
“Buhari murna ya ke ta yi, ganin cewa APC ce ta yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa, kuma kasancewa an yi zaɓen lafiya ba tare da hargitsi ba.
“Kamar yadda na ce, an yi zaɓen shugaban ƙasa a Katsina ba a kashe ko mutum ɗaya ba, kuma babu tashin hankali. Saboda haka Buhari ya na farin ciki da jin haka.
“Kun dai san a matsayin sa na shugaba mai barin gado, a ce magajin sa ɗan jam’iyyar sa ne, ai ba ma sai an ce maku ya na murna da farin ciki ba.
“Za mu yi amfani da zaɓen gwamna mu gyara ɓangaren da mu ka samu cikas a zaɓen shugaban ƙasa. Amma dai ina mai alwashin cewa APC da Dikko Raɗɗa ne za su yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Katsina.
Jam’iyyar PDP dai ta tsaida Yakubu Lado ne ɗan takarar gwamna a Katsina. Kuma ana ganin cewa za a yi gwagwagwa sosai kafin kokawar ta yi kaye.
A jajibirin zaɓen shugaban ƙasa dai an kama matasa 15 da kwamfutoci, ana zargin su da niyyar kutsen baddala sakamakon zaɓe a Katsina.
A Jihar Katsina Rundunar ‘Yan Sanda ta damƙe wasu matasa 15 da aka samu tare da sabbin kwamfutoci.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES kama matasan.
Sai dai ya ce ba gaskiya ba ne da ake yaɗa cewa an kama su da tulin ƙuri’u.
Ya ce an kama su da kwamfutoci laptop, waɗanda ake masu zargin cewa za su kutsa ne domin leƙen sakamakon zaɓe ko kuma baddala sakamakon.
Wata majiya ta bayyana wa wakilin mu cewa dukkan kwamfutocin da jami’an tsaron su ka kama a hannun matasan akwai tambarin wata jam’iyyar siyasa jikin ta.