Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu ts maida wa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi raddi, inda ta ce ƙarya ya ke yi da ya ce ya lashe zaɓe.
APC ta ce zargin an yi maguɗin da Obi ya yi ƙarya ce da kuma rashin kunya kawai.
Kakakin rundunar Festus Keyamo kuma Ministan Ƙwadago mai ƙaramar likkafa, ya yi wannan bayanin a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
A taron manema labarai da Obi ya yi a ranar Alhamis, ya ce zai garzaya kotu domin ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana cewa Bola Tinubu ne ya yi nasara.
Tuni dai manyan jam’iyyun adawa biyu kenan, PDP da LP su ka bayyana cewa za su garzaya kotu bisa zargin an tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 Ga Fabrairu.
“Peter Obi shi kan sa ya san bai ci zaɓe ba, kuma ba zai iya cin zaɓe ba, saboda yayi kamfen ɗin addinanci a tarihin siyasar Najeriya.
“Shi ma ya san ba iya cin zaɓe zai yi ba, saboda ya ɓalle daga cikin PDP, ya koma gefe a wani yanki na ƙasar nan ya yi tasiri amma ƙarya ya ke yi da ya ce ya ci zaɓe. Domin sakamako ya nuna cewa bai ci zaɓe ba.
A gefe ɗaya kuma, ADC ta kware wa PDP da LP baya, ta ce ba ta jayayya da INEC ko Tinubu.
Jam’iyyar ADC ta yi kira da PDP da LP su haƙura kawai, su daina jayayya da sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana Bola Tinubu na APC ya yi nasara.
Jam’iyyun biyu dai sun zargi INEC da tafka masu rashin adalci har ejan-ejan na su su ka fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Har ta kai su Atiku da Obi su ka yi kiran a dakatar da bayyana sakamakon zaɓe, kuma Shugaba INEC shi ma su ka ce ya sauka.
Amma ADC ta bakin Shugabar Kwamitin Dattawa, Patricia Akwashiki, ta ce ba su da wata jayayya, kuma ba su tare da PDP da LP.
Sannan kuma ta yi kira cewa a cire sunan ADC daga cikin jam”iyyun da aka ce su na jayayya, domin ba a yi shawara kafin a saka sunan ADC ba.
PDP da LP sun nemi Shugaban INEC ya sauka, Hukumar Zaɓe ta ce masu ‘kun yi kaɗan’
Jam’iyyar PDP da LP sun yi kiran gaggawa cewa Shugaban Hukumar Zaɓe, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙamin sa.
Su biyun sun yi wannan kiran ne a wani taron haɗin gwiwa na manema labarai da mataimakan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyun su ka gabatar a Abuja.
Mataimakan su ne Datti Ahmed na LP da Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, a Abuja.
A taron wanda su ka kira ranar Talata, sun kuma yi kiran a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta bayyana.
Sai dai kuma tuni INEC ta maida masu martanin cewa Yakubu ba zai sauka ba, tare da cewa duk mai wani ƙorafi ya garzaya ya bi tsarin da dokar zaɓe ta ce ya kai ƙorafin sa.
Kakakin INEC Rotimi Oyekanmi ya ce akwai hanyoyin da doka ta tsara su kai ƙorafin su, amma batun su ce wai shugaban zaɓe ya sauka, to tatsuniya ko mafarki ne kawai su ke yi.
Ko a ranar Litinin sai da INEC ta ce zargin aringizon ƙuri’u a zaɓen Ekiti ba gaskiya ba ne.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi watsi da zargin da PDP ta yi kan zaɓen Jihar Ekiti, wanda jam’iyyyar ta ce an yi aringizon ƙuri’u.
APC ce ta yi nasara a Jihar Ekiti, kuma sakamakon zaɓen jihar ne aka fara bayyanawa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe a Abuja, a ranar Lahadi.
A ranar Litinin kuma sai ejan ɗin PDP a cibiyar, Dino Melaye ya Yi kira da a soke sakamakon zaɓen Ekiti, wanda ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri’u.
Melaye tun da farko ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u 800 a zaɓen jihar Ekiti.
Shi da ɗayan ejan ɗin PDP, Emeka Iheodia, sun fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe da ke Abuja, bayan da Shugaban INEC ya ƙi biya masu buƙatar su.
Daga baya Yakubu ya maida raddin cewa babu wani abu mai kama da aringizon ƙuri’u a zaɓen Jihar Ekiti.
Ya ce babu wani aringizon ƙuri’u domin ejan ɗin jam’iyyu a Ekiti sun sanya hannun amincewa da sakamakon zaɓen.
Yakubu ya ce alƙaluman da ejan ɗin PDP ya bayyana ba daga INEC ya same su ba.
Ya ce INEC na da adadin mutum 315,058 waɗanda aka tantance, sannan daga ciki halastattun ƙuri’u su 308,171 ne. Sai kuma ƙuri’un da aka ƙi amincewa da su har 6,301.
Daga nan ya yi kira ga jam’iyyu su tuntuɓi INEC domin samun sahihin adadi, idan har wanda su ke da shi ya sha bamban.
Discussion about this post