Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ta nuna baƙin ci dangane da munmunan kisan da Boko Haram su ka yi wa masunta 30 a Gamboru Ngala, Jihar Barno.
Dukkan waɗanda aka yi wa mummunan kisan sai dai dukkan su masunta ne, kuma an ji wa wasu da dama rauni. Yanzu haka su na asibitoci daban-daban ana jiyyar su.
Jami’in Kula da ‘Yan Gudun Hijira na Najeriya, Matthias Schemale ne ya nuna wannan damuwar a cikin wata sanarwa da ya fitar, ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce lamarin da ya faru a ƙauyen Mukdolo, wanda ke kan iyakar Najeriya.
Schemale ya ce akwai fararen hular da har yanzu ba’a sake jin labarin su ba.
“Waɗanda aka yi wa munmunan kisan duk masunta ne masu kamun kifi da manoma masu neman ɗan kuɗin sayen abinci.
“Waɗanda aka yi wa mummunan kisan akwai masu gudun hijira da kuma al’ummar cikin Ƙaramar Hukumar Dikwa.”
UN ta ce mummunan kisan ya nuna irin harin barazanar da masu gudun hijira ke ciki kuma a kullum su ke fuskanta a yankunan da su ke zaune.
Schemale ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta binciken wannan mummunan ta’addanci da ya ce ake yi wa masu gudun hijira da mazauna yankunan karkara na yankin tsawon shekaru 13 a jere kenan.