Wasu bankuna a wasu sassan ƙasar nan sun dawo da biyan kwastomomi tsoffin kuɗaɗe na naira 500 da naira 1,000.
Sun fara bayar da kuɗaɗen ga masu shiga karɓar kuɗaɗe a cikin banki da kuma masu cirar kuɗaɗe a ATM.
Fara biyan tsoffin kuɗaɗen a ranar Litinin ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a makon da ya gabata, inda ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗaɗe daga nan zuwa ranar 31 Ga Disamba.
Yayin da wasu bankunan su ka dawo da biyan tsoffin kuɗaɗen, a gefe ɗaya kuma tun bayan da Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin a ranar Juma’a, har yau Babban Bankin Najeriya (CBN) bai ce komai ba. Wannan shiru da CBN ya yi kuwa ya ƙara jefa mutane cikin damuwa sosai.
A Abuja, wakilin mu ya lura da cewa a ranar Talata bankuna da dama ba su raba tsoffin kuɗaɗen ba, saboda su na jiran irin umarnin da CBN zai ba su.
Amma kuma wasu bankunan a a Legas da FCT Abuja sun biya kwastomomin su da tsoffin kuɗaɗe.
Bankuna da dama kama daga Union Bank, GTBank na Garki duk ba su bayar da tsoffin kuɗaɗen a Abuja.
Sai dai wasu bankunan kuma irin Bakin Access da Starling Bank a Abuja, sun riƙa bai wa masu cirar kuɗaɗe tsoffin Naira 500 da Naira 2,000.
Bankuna da dama waɗanda su ka ƙi dawo da biyan tsoffin kuɗaɗe har sai sun ji ko sun gani daga umarni daga CBN kuwa.
Wasu bankuna da wakilan mu su ka kewaya, irin su WEMA BAnk da Polaris duk ba su biyan tsoffin kuɗaɗe, kuma su na jiran umarni ne daga CBN.