Kwamishinan Lura da Harkokin Masu Gudun Hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana cewa an tallafa wa masu gudun hijira miliyan shida daga kuɗaɗen Gidauniyar Kuɗaɗen Zakka ta Masu Gudun Hijira, wadda UNHCR ta kafa a 2017.
Ya ce gidauniyar ta tallafa wa waɗanda aka tilasta wa baro gidajen su a ƙasashe 26 har su miliyan shida, daga 2017 zuwa yau.
UNHCR ta jinjina wa addinin Musulunci saboda muhimmiyar rawar da ya ke takawa wajen tallafa wa masu gudun hijira da tallafin kuɗaɗe a faɗin duniya.
Babban Masahawarci na Kwamishinan Lura da Masu Gudun Hijira, Khaled Khalifa ne ya bayyana wa manema labarai haka a Geneva.
“Yanzu kuma mu na so mu bijiro da riƙa kai agaji a wuraren da ƙungiyoyin addinin Musulunci ba su iya isa saboda ƙa’idojin takunkumin kuɗaɗe. Saboda mu na so UN ta faɗaɗa ayyukan ta har a cikin irin su Afghanistan, Somaliya da Musulman Rohingya.” Inji shi.
“Musulmai da Musulunci sun daɗe su na bayar da tallafi da agaji. Mu ne dai baƙin da mu ka fara wannan aikin tallafin daga baya.”
Rahoton Kuɗaɗen Gudummawar Zakkar da aka tara a 2022 ya nuna UNHCR ta tara dala miliyan 38 cikin 2022.
A wani labarin kuma, Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya taya Musulmin duniya murnar shigowar watan Ramadan.
Guterres ya yi kira da a yi amfani da alfarmar wannan wata a ƙara ƙulla danƙon zaman lafiya da ƙaunar juna a duniya.