Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya yi kira ga manyan jam”iyyun adawa biyu, PDP da LP su jingine adawa da jayayya su haɗa kai da APC a gina ƙasaitacciyar Najeriya.
Adamu ya yi wannan kiran ranar Alhamis a Abuja lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, inda ya ce a fili kowa dai ya ga yadda Bola Tinubu na APC ya lashe zaɓen ranar 25 Ga Fabrairu.
Tuni dai wasu jam’iyyun adawa kamar PDP da LP su ka ƙi amincewa da sakamakon, kuma su ka ce za su garzaya kotu.
Atiku Abubakar ya ce zai garzaya kotu, domin ya nuna wa duniya yadda aka ɗirka maguɗi.
Shi ma Peter Obi ya ce bai amince da sakamakon ba, saboda a cewar sa, shi ne ya yi nasara.
Sai dai kuma Adamu ya yi murnar nasarar da APC da Tinubu ya samu, sannan kuma ya shawarci masu jayayya su haƙure tunda sun sha kaye.
“Mu na miƙa masu hannun zumunci su zo a gina ƙasaitacciyar Najeriya.”
Tuni dai PDP da LP sun nemi Shugaban INEC ya sauka, Hukumar Zaɓe ta ce masu ‘kun yi kaɗan’
Jam’iyyar PDP da LP sun yi kiran gaggawa cewa Shugaban Hukumar Zaɓe, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙamin sa.
Su biyun sun yi wannan kiran ne a wani taron haɗin gwiwa na manema labarai da mataimakan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyun su ka gabatar a Abuja.
Mataimakan su ne Datti Ahmed na LP da Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, a Abuja.
A taron wanda su ka kira ranar Talata, sun kuma yi kiran a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta bayyana.
Sai dai kuma tuni INEC ta maida masu martanin cewa Yakubu ba zai sauka ba, tare da cewa duk mai wani ƙorafi ya garzaya ya bi tsarin da dokar zaɓe ta ce ya kai ƙorafin sa.
Kakakin INEC Rotimi Oyekanmi ya ce akwai hanyoyin da doka ta tsara su kai ƙorafin su, amma batun su ce wai shugaban zaɓe ya sauka, to tatsuniya ko mafarki ne kawai su ke yi.
Ko a ranar Litinin sai da INEC ta ce zargin aringizon ƙuri’u a zaɓen Ekiti ba gaskiya ba ne.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi watsi da zargin da PDP ta yi kan zaɓen Jihar Ekiti, wanda jam’iyyyar ta ce an yi aringizon ƙuri’u.
APC ce ta yi nasara a Jihar Ekiti, kuma sakamakon zaɓen jihar ne aka fara bayyanawa a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe a Abuja, a ranar Lahadi.
A ranar Litinin kuma sai ejan ɗin PDP a cibiyar, Dino Melaye ya Yi kira da a soke sakamakon zaɓen Ekiti, wanda ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuri’u.
Melaye tun da farko ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u 800 a zaɓen jihar Ekiti.
Shi da ɗayan ejan ɗin PDP, Emeka Iheodia, sun fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe da ke Abuja, bayan da Shugaban INEC ya ƙi biya masu buƙatar su.
Daga baya Yakubu ya maida raddin cewa babu wani abu mai kama da aringizon ƙuri’u a zaɓen Jihar Ekiti.
Ya ce babu wani aringizon ƙuri’u domin ejan ɗin jam’iyyu a Ekiti sun sanya hannun amincewa da sakamakon zaɓen.
Yakubu ya ce alƙaluman da ejan ɗin PDP ya bayyana ba daga INEC ya same su ba.
Ya ce INEC na da adadin mutum 315,058 waɗanda aka tantance, sannan daga ciki halastattun ƙuri’u su 308,171 ne. Sai kuma ƙuri’un da aka ƙi amincewa da su har 6,301.
Daga nan ya yi kira ga jam’iyyu su tuntuɓi INEC domin samun sahihin adadi, idan har wanda su ke da shi ya sha bamban.
A Jihar Legas ma PDP ta ƙi amincewa da sakamakon yawan ƙuri’un Peter Obi a Legas.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta amince da sakamakon yawan ƙuri’un da jam’iyyar LP ta Peter Obi ta samu a Jihar Legas ba.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Legas, Tunji Shelle wanda kuma shi ne ejan ɗin PDP wurin tattara sakamakon zabe a Yaba, Legas, ya ce “an yi ƙumbiya-ƙumbiya gabaɗayan aikin tattara ƙuri’un.”
“Ban amince da sakamakon zaɓen ba, kuma na ɗauki wannan matsaya ce a madadin jam’iyyar da na ke wakilta, PDP.” Haka Shelle ya bayyana wajen tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin.
“Ban amince da sakamakon da LP ta samu ba, ba wai don ba mu yi nasara ba. Amma saboda an saye waɗanda aka saye aka yi mana ƙumbiya-ƙumbiya.”
Peter Obi na LP dai ya lashe yawan ƙuri’un jihar Legas har 582,454, shi kuma Bola Tinubu na APC 572,606.
Atiku Abubakar na PDP ya samu 75,750.
“Ba na jin INEC ta bayar da kyakkyawan horon aikin zaɓe ga ma’aikatan wucin-gadin da ta ɗauka. Saboda a gaskiya ba mu shirya wa fara aiki da na’urar tantance masu rajistar zaɓe ba, wato BVAS. Saboda a wurin tantancewar ne ake yin amaja. Da yawan sakamakon zaɓen duk ba a ma loda su a BVAS ɗin. Amma haka aka fitar da sakamako.”
Ya ce kamata ya yi BVAS ya tsaftace aikin zaɓe, amma maimakon haka, sai ma ya ƙara maida hannun agogo baya.
Discussion about this post