Wasu tubabbun ‘yan bindiga sun roki afuwar ‘yan Najeriya kan irin rawan da suka taka wajen tada zaune tsaye a kasar nan.
Maharan da suka kai mutum 542 sun roki afuwar ‘yan Najeriya ranar Asabar a karamar hukumar Kwami jihar Gombe.
“Muna rokon dun mutane, da wadanda ke kauyukan mu da gwamnatocin jihohin mu da su yi mana afuwa su yafe mana.
Daya daga cikin tubabbun Boko Haram/ ISWAP Muhammad Abba ya ce sun yi nadamar abin da suka aikata.
“Mun yi rantsuwar mubaya’a ga kasar mu mu zauna lafiya da kaunar juna. Muna Kuma da masaniyar la’anar dake tattare da irin rantsuwar da muka yi da Kur’ani Mai Girma idan muka karya wannan rantsuwa da muka yi.
“Fushin Allah da la’ana na tattare da duk Wanda ya bijire wa rantsuwar da muka yi sannan idan ma mutum ya kubuta daga shiga hannun jami’an tsaro babu kubuta daga fushin Allah.
“Yanzu da za mu koma gida garurruwan mu za mu tabbatar cewa mun yi aiki da horon da muka samu domin inganta zaman lafiya.
Ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan Shirin horas da tubabbun Boko Haram/ISWAP sannan ya tabbatar cewa za su yi aiki domin ganin Shugaban kasa bai yi dana sanin yin haka ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta rawaito cewa bayan an kammala horos da tubabbun Boko Haram/ISWAP 594 za a mai da su garurruwan su.
Kwamandan dakarun Najeriya da ke kula da horas da tubabbun ‘yan bindigan kwanel Uche Nnabuihe ya ce mutum uku daga cikin tubabbun Boko Haram/ISWAP ‘yan kasar Nejar ne sai wani mutum daya dan kasar Chadi.
Ya kuma ce wasu mutum shida daga cikinsu Kiristoci ne.
Nnabuihe ya ce mutum biyar daga cikin su daga jihar Adamawa suke mutum 495 daga jihar Borno, 16 daga jihar Kano, uku daga Gombe,16 daga Yobe, 13 daga Kaduna sai daya daga jihar Kogi.
Ya ce sauran sun hada da mutum 12 daga Bauchi, biyar daga Jigawa, biyar daga Katsina, hudu daga Kebbi, daya daga Nasarawa, daya daga Filato da biyu daga Zamfara.