Jami’an tsaro sun Kama wani ɗan ina-da-aiki mai suna Onyebuchi Ezeh, bayan ya yanke al’aurar wata gyatuma mai shekaru 72 domin haɗa laƙanin tsafin yin kuɗi lokaci ɗaya.
Ba al’aurar tsohuwar kaɗai Ezeh ya yanke ba, ya kuma guntuli ‘yan yatsun ta, ya reɗe kunnuwan ta, kuma ya gutsure mata kan nonuwa biyu.
Mummunan al’amarin ya faru ne a Jihar Anambra, ranar Alhamis, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Kwamishinar Harkokin Mata ta Anambra, Chidinma Ikeanyiownu ta bayyana ta bakin kakakin, Ife Obinabo.
Ta ce amma dai an ceci ran wannan gyatuma wadda aka daddatsi sassan jikin na ta.
Gyatumar dai haifaffiyar garin Umunze ce a cikin Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa.
“Jama’a sun taras an yi wa wannan gyatuma mummunar aika-aika a ranar Alhamis, lokacin da ta yi kururuwar neman ceto.
Ɗan ina-da-aiki ne mai taya ta ɗibar kwakwar man ja tare da wasu mutane biyu, su ka danne ta a gidan ta da ƙarfin tsiya, su ka yanki sassan jikin ta.”
Ya bayyana da bakin sa cewa sun ciri sannan jikin na ta ne domin bai wa wani matsafi ya haɗa masu laƙanin yin kuɗi lokaci ɗaya.
Ezeh dai ya zo hannu, kuma ya ce shi ɗan asalin Abakaliki ne, ya ce ya na taya tsohuwar ɗebo mata kwakwar man ja ce.
Tsohuwar dai a yanzu ta na Asibitin Koyarwa na Odumegwu Ojukwu da ke Awka, ana fama jiyyar ta.
Yayin da ake tsare da Ezeh a Ofishin ‘Yan Sandan CID da ke Jihar Anambra, ana ci gaba da bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Anambra ya nuna takaici tare da yin alwashin kamo sauran masu laifin, domin a gurfanar da su.