Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya maida wa tsohon gwamna Kaduna Ahmed Makarfi martani kan wasu kalamai da tsohon gwamnan yayi game da gwamnatin El-Rufai.
El-Rufai ya zargi tsohon gwamna Maƙarfi da rashin taɓuka abin azo a gani a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kaduna.
El-Rufai ya ce ” mun san irin kuɗaɗen da gwamnatin Kaduna ta samu a lokacin gwamnatin Makarfi, amma abinda gwamnatin kawai ta iya yi sannan ta yi alfahari da shi shine, ƴar ƙumbular gadan sama da ta yi, wanda ba wani abin a zo a gani bane.
El-Rufai ya ce an tafka taɓargaza da harƙalla a wannan gwamnati amma kuma da mun yi shiru saboda kawai don a bar kaza cikin gashin ta, amma kuma tunda abin ya zama haka, El-Rufai ya ce zai fito ya fasa kwan, ƴan Kaduna su san ko ma me ya faru da kuɗaɗen su ƙarkashin gwamnatocin baya.
Tsakanin El-Rufai da Makarfi
Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa zai iya yin rantsuwa cewa bai ɗauki kwabon jihar Kaduna da sunan sata ba ya yi gaban kan sa da su ba.
A wata hira da yayi da Talbijin mallakar jihar KSMC El-Rufai ya ce burin sa shine ya gyara garin Kaduna ta yadda idan ka shigo cikin gari ba za ka taka kasa ba ko ina titi ne da hasken wutan lantarki.
” Buri ma shekarar ne in kayata jihar Kaduna, Zaria, Kafanchan, da sauran manyan garuruwan jihar.
” Zan rantse a ko ina ne cewa ban saci ko kwabon mutanen Kaduna ba, amma ida gwamnonin baya sun isa su zo su rantse suma.
” Ni ba irin gwamnonin nan ne da suka sace kuɗin jiha suka gina gida a Jabi road bane, ko kuma waɗanda suka yi wuf suka arce da kuɗin kuɗaɗen jihar Dubai. Gida na ɗaya tilo a Kaduna, kuma tun da na zama gwamna kuma ita ce dai har yanzu.
‘ Waɗanda suka wafce kuɗin Kaduna suka zama masu kudi yanzu, suka mallaki kantamakantaman gidaje a jihar ba ƴaƴan Dangote bane ko Ɗantata, mun san su tun a jami’a. Babu wani abu da bamu sani ba.Su fito su rantse ba kuɗin talakawan kaduna bane suke bushasharsu da su.
Amma ni gaskiya ta ita ce ban ɗauki ko sisin mutanen Kaduna ba. Mu tara kuɗi, mun ciyo bashi amma duka mun yi aiki ne da su, kuma muna kan aikin ne har yanzu.
Discussion about this post