Kotun Koli ta ce a ci gaba da amfani da hadahada na kasuwanci da tsoffin takardun kuɗin har zuwa 31 ga Disambar 2023.
Hakan na kunsje a hukuncin da kotun ta yanke ranar Juma’a a Abuja.
Duka alkalai bakwai da suka yanke hukuncin sun e Buhari ya karya dokar kasa ƙaƙaba wannan umarni da yayi da kuma yin biris da umarnin kotu tun a 8 ga Faburairu.
Maishari’a Emmanuel Agim da yayi magana a madadin Alkalai bakwai da suka yanke hukuncin ya ce ba ya ga karya dokar kasa da Buhari yayi a wajen wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗin, Buhari nuna karfin iko irin na ‘kama karya’ a kan ƴan Najeriya.
Bisa ga wannan hukunci, za a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi daga yanzu har zuwa karshen shekarar 2023, wato watan Disamba.