Kotun Ƙoli ta ƙaryata rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta buga cewa Cif Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola ya yi shigar-burtu a birnin Landan, ya yi ganawar sirri da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Peoples Gazette ce ta ruwaito labarin a ranar Alhamis, inda ta wallafa cewa an ga Ariwoola a kan keken guragu zaune ana tura shi, za a shiga da shi inda Tinubu ya ke.
Sai dai kuma a wata tattaunawa da Kakakin Yaɗa Labaran Kotun Ƙoli, Festus Akande ya yi da PREMIUM TIMES, ya ce ƙarairayi da labarin bogi ne kawai Peoples Gazette ta buga.
Jaridar ta ce Ariwoola ya tafi Ingila ranar 11 ga Maris domin su yi mahaɗa da Tinubu a can.
Sai dai Akande ya ce “jaridar ƙarya ta ke yi, domin Cif Jojin Najeriya bai je Ingila ba, ya na nan Najeriya, kuma shi ne ya jagoranci taron Hukumar NJC a ranakun 16 da 17 Ga Maris.”
Akande ya ce Ariwoola ya je Landan a ranar 18 Ga Maris bisa rakiyar Sakataren NJC, Gambo Saleh, domin a duba lafiyar sa.
“Ya dawo gida Najeriya a ranar 23 Ga Maris, kuma ya yi aiki a ofis har ƙarfe 8 na dare sannan ya tashi.”
Akande ya ce kafin Ariwoola ya tafi Landan ɗin, sai da ya sanar wa Shugaba Muhammadu Buhari.
Wakilin mu ya ga lokacin da Ariwoola ya fita daga ofis ya shiga Masallacin Juma’a a ranar Juma’a, 24 Ga Maris, a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Amma a ranar Alhamis Peoples Gazette ta ce Cif Jojin Najeriya ɗin ya na Landan, ya na ganawar sirri da Tinubu.
Shi ma Tinubu ya ƙaryata labarin ya yi ganawar sirri da Cif Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola.
Bayo Onanuga ya ce har yanzu Tinubu ya na Paris, bai ma ƙarasa Landan ba tukunna.
Tinubu ya bar Najeriya ranar 21 Ga Maris, ya tafi Paris, daga can zai wuce Landan da kuma Saudi Arabiya domin ya yi Umrah.
Discussion about this post