Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano, ta bayar da belin ɗan majalisar tarayya dake wakiltar Doguwa a majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa.
Kakakin kotunan Kano Baba Jibo, ya ce daman hakan yana kan tsari sannan a bisa doka. Amma ya ce za a ci gaba da sauraron shari’ar zargin kisan wasu mutum biyu da ake yi masa.
Ya ce Kotun ta kalubalanci hukumar ‘yan sanda saboda kai Doguwa kotun da bata da hurumin sauraron irin laifin da ake tuhumarsa da shi.
Ƴan sandan na zargin sa da hannu a harbin wasu mutane uku da bindiga kwana ɗaya bayan kammala a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudunwada dake jihar Kano.
Ana kuma tuhumar ɗan majalisar da laifin kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu guda takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.
Mutane da dama sun yi tofin Allah-tsine dyk da cewa ba a tabbatar da zargin da ake yi wa ɗan majalisar ba. Sannan bayan haka an zarge shi da sa wa a cinna wa wasu gine-gine wuta yana zaune ya na kallo da kuma zargin dabanci.
Discussion about this post