Daga cikin manyan ‘yan siyasar Arewa da su ka faɗi zaɓe, akwai guda uku waɗanda za su daɗe su na cizon yatsa saboda takaici. Wataƙila ma har sai sun guntule yatsun ba su sani ba, saboda gushewar tunani a kuma haushi.
Na farkon su shi ne Gwamna Samuel Ortom, wanda tsohon ɗan aiken sa ya kayar da shi zaɓen Sanatan Jihar Benuwai.
Akwai kuma Sanata Kabiru Gaya na Jihar Kano, wanda Kawu Sumaila ya kayar a zaɓen Sanatan Kano ta Gabas, da ratar ƙuri’u fiye da 100,000.
Sai na uku shi ne kayen da Sanata Adamu Aleiro ya yi wa Gwamna Abubakar Bagudu na Kebbi, a zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya.
Aleiro na PDP ya samu ƙuri’u 126,588, shi kuma Gwamna Bagudu ya samu 92,389. Akwai ratar fiye da ƙuri’u fiye da 34,000 a tsakanin su.
Da farko dai Sanata Adamu Aliero ne na PDP ya kayar da Atiku Bagudu na APC, a Zaɓen Sanatan Kebbi ta Tsakiya.
Aliero ya samu ƙuri’u 126,588, shi kuma Bagudu ya samu 92,389.
Aliero wanda ya yi nasara ɗan APC ne, amma saɓani tsakanin sa da Bagudu ya kai shi ga ficewa ya koma PDP, inda ya tsaya takarar sanata, kuma ya yi nasara.
Salsalar Rikicin Gwamna Bagudu Da Sanata Aleiro:
Premium Times ta buga wannan labari cikin watan Janairu, 2022.
2023: Yadda yunƙurin ƙaƙaba Minista Malami takarar gwamna ya haddasa wa APC rikici a Jihar Kebbi:
Wani shiri da aka ce Gwamna Atiku Bagudu ke yi domin ya ƙaƙaba Ministan Shari’a Abubakar Malami matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kebbi kai tsaye a zaɓen 2023, ya haifar da rikici a cikin APC a Jihar Kebbi.
Masu yi wa wannan shiri bore sun tuma tsalle gefe ɗaya sun yaga rigar APC, sun ɗauki ta su guntuwar rigar, sun yafa wa tsohon Gwamnan Jihar, Adamu Aliero a matsayin shugaban su, ko jagoran adawar su. Aliero dai Sanata ne mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya.
Lamari ya ƙara lalacewa kwanan nan, inda rikici ya kunno kai yayin da Aliero da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa, su ka yanke shawarar buɗe sabuwar Sakateriyar APC ta su ta ‘yan adawa. Hakan na nufin buɗe ofishin jam’iyyar ɓangaren Aliero, mai adawa da shugabannin APC na Kebbi masu bin umarnin Gwamna Bagudu.
Wani abin ɗaure kai shi ne ginin da su Aliero su ka buɗe ta su sakateriyar APC ta ɓangaren su, gini ne mallakar Bello Bagudu, yayan Gwamna Abubakar Bagudu. Ginin ya na kan titin Emir Haruna Road, a babban birnin Jihar, wato Birnin Kebbi.
Sai dai kuma haƙar su Aliero ba ta cimma ruwa ba, domin jami’an tsaro sun tarwatsa gungun magoya bayan su, a lokacin da aka je buɗe sakateriyar.
Neman A Yi Zaɓen ‘Yar-tinƙe Wajen Fidda Ɗan Takarar Gwamna:
Aliero dai ya samu tarba daga ɗinkin ɗimbin magoya bayan su a wurin taron, kafin ‘yan sanda su tarwatsa su.
Ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta yi amfani da tsarin zaɓen ‘yar-tinƙe ne wajen fidda gwanin takara, domin a ba kowa damar zaɓen wanda ya ke so ya tsaya masa. Haka ma irin wannan zaɓe ya ce za a yi yayin zaɓen shugabannin jam’iyya.
Aliero ya ce ‘yan siyasar da ke tsoron irin wannan zaɓe, sun san ba su tsinana wa al’ummar yankunan karkara komai ba.
Duk da dai Sanata Aliero bai bayyana sunan kowa ba, amma masu lura da siyasar Kebbi sun tabbatar cewa da Gwamna Bagudu ya ke, shi da Minista Malami.
A wurin gangamin buɗe ofishin dai Aliero ya ci gaba da bayyana irin ayyukan da ya yi wa al’umma. Amma kuma ya samu goyon bayan jama’ar da ke wurin da ke so a yi zaɓen ‘yar-tinƙe yayin fidda gwani, kamar yadda Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya bada damar a yi. Wato ba su son a bi tsarin zaɓe na amfani da wakilan jam’iyya kenan.
Wannan hatsaniya ta Kebbi ta taso ne bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa hannu kan Sabon Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda da farko ya ce zaɓen kai-tsaye kaɗai za a yi wajen fitar da ɗan takara, ba tsarin zaɓe wanda wakilan jam’iyya wato ‘delegates’ ke yi ba.
To amma yanzu Majalisa ta cire wannan ƙudiri, ta ce za a iya bin tsari ɗaya daga cikin uku: Ko zaɓen kai-tsaye, ƙato bayan ƙato, zaɓe tsarin amfani da wakilan jam’iyya (delegates), ko kuma ta hanyar tsayar da ɗan takara ba tare da zaɓe ba, idan kowane ɓangare na ‘yan jam’iyya sun amince da hakan.
Yayin da ‘Yan Majalisa ke so a bi tsarin zaɓen kai-tsaye, gwamnoni kuma sun fi so a ci gaba da bin tsarin amfani da wakilan jam’iyya a fidda gwanin takara. Lamarin da kowa ke ganin saboda gwamnonin ne ke yadda su ka ga dama da wakilan zaɓen a lokacin. Kuma sai wanda gwamna ke so za su zaɓa.
Bayan an tarwatsa gungun magoya bayan su Aliero, kakakin su Sani Dododo ya shaida PREMIUM TIMES HAUSA cewa rikicin APC a Kebbi ya samo asali ne tun daga lokacin da wasu suka ji haushin yadda gwamna ya yi amfani da wakilan zaɓe aka maida su saniyar-ware yayin zaɓen shugabannin jam’iyya a mazaɓu da ƙananan2aa hukumomi. Waɗannan shuagabanni kuma dama su ne ke yin zaɓen fidda gwani.
Dododo ya ce an yi wani taron masu ruwa da tsaki na APC a Jihar kafin a yi zaɓen shugabannin mazaɓun da na ƙananan hukumomi a jihar.
“Gwamna da Sanatoci uku da ‘Yan Majalisar Tarayya takwas sun halarta. Haka ‘Yan Majalisar Jiha da Mataimakin Gwamna duk su na wurin, kuma aka amince cewa za a cimma yarjejeniyar fidda shugabanni ce ba tare da zaɓe ba.
“Kuma aka amince cewa za a sake barin shuagabanni da ke kan mulki su ci gaba, sai fa inda ke da gurbin wanda ke kai ya mutu ne, to a nan za a cike gurbin sa da wani.
“Aka amince cewa za a kai sunayen waɗanda su ka mutu da shuagabannin da su ka canja sheƙa ko rashin lafiya ta hana su riƙe muƙamin su. Idan aka kai sunayen su ofishin jam’iyya, sai a tantance waɗanda za su maye gurbin su. Wannan ita ce yarjejeniyar da aka cimma.” Inji Dododo.
Yadda Gwamna Bagudu Ya Baddala Sunayen Shugabannin APC A Mazaɓu Da Kananan Hukumomin Kebbi -Sani Dododo:
A hirar da PREMIUM TIMES, Dododo ya ce Bagudu ya damalmala lissafin sunayen, inda a Ƙaramar Hukumar Argungu kaɗai ya cire sunayen mutum 101 na shugabannin jam’iyyar APC, ciki kuwa Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Argungu, Sakataren Jam’iyya da Ma’aji. Ya ce waɗanda aka cire ɗin duk magoya bayan Aliero ne.
Ya ce irin wannan ƙarfa-ƙarfa da Bagudu ya yi, ya maida su saniyar-ware ce ta sa su ma suka buɗe ba su ofishin daban.
Ya ce sun sanar wa ‘yan sanda za su yi taron su. Kuma saboda gudun tashin hankali ya sa su ka buɗe na su ofishin a wani wuri daban. Amma kuma sun zargi ‘yan sanda da nuna goyon bayan ɓangaren Gwamna Bagudu.
Isa Assalafy kuwa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Gwamna Bagudu ba shi da laifi, duk waɗanda aka cire ɗin mutanen su ne daga mazaɓu su ka cire su. Ya shawarci ɓangaren Aliero su koma can daga mazaɓu su gyaro ta tsakanin su da mutanen karkara.
Sai dai kuma duk wannan rikici wani sharar daji ne tsakanin masu don tsayar da Minista Malami takara da kuma su Aliero waɗanda ba su yarda da hakan ba.
Ko a cikin Satumba, 2021, Shuagaban Kwamitin Dattawan APC na Jihar Kebbi Sani Zauro, ya bayyana cewa “idan Bagudu ya kammala shekarun sa takwas, sai miƙa takara ga Minista Malami lokacin zaɓen 2023. Kuma gwamna ɗin ne da kan sa ya tabbatar mana da haka.”
Dama kuma dalilin ƙoƙarin ɗora Malami ne ya haifar da cire Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Sani Kamba.
Sai dai kuma ko shakka babu wannan rikici ya haifar wa Malami cikas da koma-baya a ƙoƙarin sa da kuma ƙoƙarin da ake yi masa ya hau kujerar Gwamnan Kebbi.
Discussion about this post