Fitacciyar ‘yar taratsin kishin talakawa Aisha Yesufu ta ɗaura banten rigima da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, a kan goyon bayan da Obi ɗin ke wa ɗan takarar gwamnan jihar Enugu na LP, Chijioke Edeoga.
Yayin da zaɓen gwamna ya gabato a ranar 18 ga Maris, Obi ya shiga shafin sa na Tiwita inda ya yi kira da zaɓi dukkan ‘yan takarar gwamna da LP ta tsayar a faɗin ƙasar nan. Kuma su zaɓi dukkan ‘yan takarar majalisar jihohi na LP.
Cikin waɗanda ya fito ya ambaci sunan su ƙuru-ƙuru har da Rhodes Vivor na Legas, Chijioke Edeoga na Enugu, Patrick Dakum na Filato da kuma Alex Otti na Abiya, sai Ken Pela na Delta.”
Sai dai kuma bayan ya watsa wannan sanarwa a shafin sa Tiwita, sai Aisha Yesufu, wadda ita ma ‘yar jam’iyyar LP ce, ta ƙi yarda da cancantar ɗan takarar Jihar Enugu, Edeoga.
“Kada Allah ya sa na koma irin abin da na ke fafutikar canjawa. Ba zan taɓa ɗaukar rashin cancanta ba, muddin akwai nagartacce a kusa ko a nesa.” Haka ta bayyana a kan cewa ba za ta goyi bayan Edeoga ba.
Maimakon haka, sai A’isha Yesifu ta bayyana goyon bayan ta ga ɗan takarar APG, Frank Nweke.
“Frank Nweke shi ne ya fi cancanta ya zama Gwamnan Jihar Enugu. Wanda ya san darajar jama’a ya kamata a zaɓa, ba wanda kan sa kaɗai ya sani ba.” Inji A’isha.
A’isha Yesufu dai ta kasance ‘yar sahun gaba ta kamfen ɗin takarar shugabancin ƙasa da Peter Obi ya yi.
A jihar Enugu dai LP ta lashe ‘yan majalisar wakilai ta ƙasa guda bakwai daga cikin takwas na jihar. Sannan kuma LP ce ta lashe zaɓen sanatoci biyu na jihar da aka gudanar.
Jihar Enugu dai jiha ce ta PDP. Kuma tun 1999 PDP ɗin ce ke lashe zaɓukan da ake gudanarwa a Jihar Enugu ɗin.