Jam’iyyar APC ta naɗa gaggan lauyoyin da za su yi mata gogayya da lauyoyin Atiku Abubakar na PDP da na Peter Obi, ɗan takarar LP.
APC za ta yi ƙoƙarin kare kan ta ne daga zargin maguɗin da Atiku da Obi su ka ce an yi masu.
Sun garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, sun shigar da tankiyar ƙin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta bayyana cewa Bola Tinubu na APC ne ya lashe zaɓen.
Cikin wata sanarwa da Mashawarcin Harkokin Shari’a na APC ya fitar, Ahmad El-Marzuq ya bayyana cewa gaggan lauyoyin da APC ta ɗauka masu hazaƙa ne kuma gogaggu, sannan ƙwararru wajen sanin batun ɗaukaka ƙararrakin zaɓe, dokar ƙasa da kuma faɗi-tashin gwagwarmayar shari’u a kotuna daban-daban.
Ya ce APC ta ɗauki Manyan Lauyoyi 13, wato SAN, waɗanda za su yi aiki a ƙarƙashin sanannen lauya Lateef Fagbemi.
Sauran sun haɗa shi kan sa El-Marzuq ɗin, Sam Ologunorisa, Rotimi Oguneso, Olabisi Syebo, Gbotega Oyewole, Muritala Abdulrasheed da Aliyu Saiki.
Sauran sun haɗa da Tajuddeen Oladoja, Pius Akubo, Oluseye Opasanya, Suraju Saida da Kazeem Adeniyi.
Wannan jarida ta tabbatar da cewa shi ma Atiku ya kafa gaggan lauyoyin da ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa, ya kafa gaggan lauyoyin da ya bai wa aikin ƙwato masa nasarar da ya yi iƙirarin cewa shi ne ya ci zaɓen ranar 25 Ga Fabrairu.
Ya ce ya na so su ƙwato masa haƙƙin sa, kuma hakan a cewar sa zai zamo wani ginshiƙin ƙarfafa dimokraɗiyya a Najeriya.
Yayin da ya ke wa lauyoyin jawabi a hedikwatar kamfen ɗin sa, lauyoyin waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin Babban Lauya Joe Gadzama, Atiku ya shaida masu cewa su iyakar ƙoƙarin su wajen ƙwato masa haƙƙi, ba don shi kaɗai ba, kuma ba don PDP ba, sai don hakan zai ƙara wa dimokraɗiyya daraja, kuma zai ƙara tsaftace tsarin zaɓe, kuma hakan zai zama alheri har ga yaran da za a haifa shekaru masu zuwa.
Lauyoyin da Atiku ya ɗauka sun haɗa da Chris Uche, Paul Usoro, Tayo Jegede, Mike Ozekhome, Mahmood Magaji, Joe Abraham, Chukwuma Umeh, Garba Tetengi da kuma Emeka Etiaba, waɗanda dukkan su Manyan Lauyoyi ne, wato SAN.
Sauran sun haɗa da Goddy Uche, Maxwell Gidado, A.K Ajibade, O. M Atayebi, Nella Rabana, Paul Ogbole, Nuremi Jimoh da kuma Abdul Ibrahim, su ma duk manyan lauyoyi ne, SAN.
Idan ba a manta ba, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bai wa Atiku Abubakar da Peter Obi na LP iznin binciken ƙwaƙwaf kan na’urorin BVAS da aka yi zaɓen shugaban ƙasa a kan zargin an yi amfani da BVAS ɗin aka yi masu maguɗi.
Discussion about this post