Jam’iyyun adawa a jihar Kano na zargin gwamnatin jihar da shigo da riƙaƙƙun ƴan daba daga kasashen dake makwabtaka da kasar nan domin su hargitsa zaben gwamna da za a yi ranar 11 ga Maris.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta samu labarin shirin da wasu ‘yan siyasa ke yi na shigo da ‘yan jagaliya da hatsabiben ƴan sara-suka daga kasashen waje domin su hargitsa zaben ranar 11 ga Maris.
Maimagana da yawun jami’yyar NNPP ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta shigo da wadannan ‘yan jagaliya ne domin hargitsa zaben da za a yi domin suna hangen faɗi kasa warwas.
“Muna da masaniyar yadda gwamnatin Ganduje ta shigo da ‘yan jagaliya daga kasashen Chadi da Jamhuriyyar Nijar da wadanda aka kawo su daga jihohin Kaduna da Katsina domin su hargitsa zaben gwamna da za a yi.
“Hukumar tsaro na DSS da rundunar ‘yan Sanda na kasa na da masaniyar haka sannan da yadda aka rarraba su zuwa duka kananan hukumomin jihar 44 domin a tada zaune tsaye.
“Ya kamata gwamnatin Najeriya da dukkan ‘yan Najeriya su sani cewa duk wani tashin hankali da aka samu a ranar zabe a nemi gwamna Ganduje da maƙarraban sa da masu mara masa baya da suka haɗa da daraktan DSS na Kano da wasu jami’an tsaro da duk ya kamata a yanzu a ce sun yi ritaya ne shekara daya da ya gabata amma aka ajiye su don su yi wannan aiki.
“Ya kamata jami’an tsaro su mike tsaye domin tarwatsa mugun Shirin da wadannan mutane ke kitsa wa don cero mutanen jihar Kano.
Saidai kuma ita ama gwamnatin Kano na zargin cewa ƴan Kwankwasiyya ne ke shirya yadda za su kawo tashin hankali a Kano a lokacin zaɓe.
Kakakin gwamnatin jihar Muhammad Garba a lokacin da yake tattaunawa da jaridar ‘Daily Trust’ ya ce gwamnati ta samu bayanan sirri daga sannan kuma daga jami’an tsaro cewa jami’yyar NNPP ne ke shirin kawo tashin hankali a jihar a lokacin zaɓen ranar Asabar.
Garba ya ce jami’yyar NNPP ta gano cewa an gano shirin da take yi ne ya sa take yin rufa-rufa ta hanyar yin mummunar hari.
A karshe rundunar ƴan sandan jihar ta ce ba za tayi kasa a guiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu yana kokarin tada zaune tsaye a jihar a lokacin zaɓe.
Ta ce za ta baza jami’anta a ko’ina a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro a lokacin.