Kotun Ƙoli a Abuja ta bayyana cewa Sanata Rufai Hanga ne halastaccen wanda ya yi nasara a zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya, ba Ibrahim Shekarau na PDP ba.
Kotun Ƙoli ta haramta nasarar kujerar ga Ibrahim Shekarau, tsohon Gwamnan Jihar Kano.
Shekarau tun da farko ya tsaya takarar sanata a ƙarƙashin NNPP, amma sai ya fice ya koma PDP kafin a kai ga zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Sai dai kuma lokacin da sakamakon zaɓe ya fito, maimakon a ga sunan Rufai Hanga wanda NNPP ta maye gurbin Shekarau da shi, sai aka ga sunan Shekarau a NNPP ɗin, bayan tuni ya rigaya ya koma PDP.
A ranar 7 Ga Maris da INEC ta bayar da satifiket na shaidar lashe zaɓe dai Shekarau bai ma halarta ba.
Yayin da Kotun Ƙoli ta ke yanke hukunci, ta jaddada cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da na Kotun Ɗaukaka Ƙara kan halaccin Rufai Hanga daidai ne.
Manyan Alƙalai biyar ne su ka yanke hukuncin, wanda Babbar Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ta rubuta, shi kuma Babban Mai Shari’a Emmanual Agim ya karanta.
Hukuncin ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa INEC ta ɗaukaka ƙarar rashin amincewa da sunan Hanga, tunda dai Shekarau ya fice daga NNPP, bai yi takara a jam’iyyar ba.
Idan za a tuna, Shekarau ya fice daga NNPP ya koma PDP cikin Satumba, 2022.
NNPP ta maye gurbin sa da sunan Hanga, wanda a zaɓen Sanata ya sami ƙuri’u 456,787.
Sai dai kuma yayin da sakamakon zaɓe ya fito, sai INEC ta rattaba sunan Shekarau, maimakon na Hanga.
Shi ne a yanzu Kotun Ƙoli ta maida wa Rufai Hanga ɗin nasarar sa.
Babu wani ruɗani:
Ficewar Shekarau Daga NNPP Da Yadda Hakan Ya Yi Masa Asarar Kujerar Sanata:
1. Shekarau ya tsaya takarar sanata a NNPP.
2. Daga baya ya fice, ya yi sanarwar ya koma PDP.
3. Amma bai sanar da INEC da wuri a rubuce ba, sai da lokacin canja sheƙa ya wuce.
4. INEC ba za ta iya canja sunan sa ba kenan. Sai dai kotu.
5. NNPP ta kai wa INEC sunan Rufai Hanga.
6. Hanga aka zaɓa a NNPP, ba Shekarau ba.
7. Shi ya sa Kotun Ƙoli ta maida wa Hanga kujerar sa.
8. Tunda ba zaɓen fidda-gwani ba ne, ballanata a bai wa wanda ya zo wa Shekarau na biyu.