A tarihin siyasar Najeriya, mafiya yawan gwamnoni na tsoron bai wa mataimakan su takarar gwamna a lokacin da wa’adin gwamna ya ƙare. Ba komai ake gudu ba, sai butulci, saboda Bahaushe ya rigaya ya camfa ɗan Adam, ya kira shi butulu.
An ga irin haka a Jihar Zamfara, inda Ahmed Yarima ya bai wa Mamuda Shinkafi ‘halifancin’ gwamna. Amma tun tafiya ba ta yi nisa ba su ka yi baram-baram. Lamarin da ya zama gaba a tsakanin su.
A jihar Kano kuwa siyasar birnin Dabo da jihar baki ɗaya cike take da tarihin butulci tsakanin ‘yan siyasa. Amma dai mafi muni na ‘yan shekarun nan, shi ne irin butulcin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi wa Kwankwaso.
Rashin jituwar da ke tsakanin Ganduje da Kwankwaso a siyasance, ta kai abin ishara ga duk wanda ke tsoron a yi masa butulci.
Lokacin da Ganduje ya zama Gwamna, a wani taro ya yi wa Kwankwaso godiya a matsayin sa na ubangidan sa, wanda dalilin tsayar da shi takara ne ya zama Gwamna.
Ganduje ya nuna cewa bai taɓa tsammanin zai zama gwamna ba, kasancewar sa wanda ya tashi a ruga ya na gararambar kiwo, ya na tafiya da karnai.
Sai dai abin mamaki, tun kafin Ganduje ya daɗe kan mulkin Gwamna a Kano, ya samu saɓani da ubangidan sa Kwankwaso. Babu wuri ko lokacin da za a bayyana irin gabar da ke tsakanin su. Butulci kenan.
Butulcin da Ganduje ya yi wa Kwankwaso ya yi munin da ta kai ya riƙa kwashe mutanen Kwankwaso ya na ba su muƙamai. Haka lamarin ya kasance, har adawa da gaba tsakanin su biyu ta kai Kwankwaso ya ɗauki tsawon lokaci bai shiga Kano daga Abuja ba, a lokacin da ya ke Sanata.
A zaɓen 2019 kuwa nan ne aka yi ‘bare duniya, ko lahira kada Allah ya haɗa mu tsakanin su biyun da magoya bayan su. An yi zaɓen gwamna a yanayin da ta kai an yi ‘inkwankilusib’, zaɓen da har yau a duk duniya magoya bayan Ganduje ne kaɗai ke halasta ‘inkwankilusib’ ɗin da aka kayar da Abbba Gida-gida, ɗan takarar Kwankwasiyya a lokacin.
Yanzu da zaɓen 2023 na gwamnan Kano ya zo, Ganduje ya tsayar da manya kuma guma-guman da su ka gantsara wa Kwankwasiyya a Gama, wato Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna da Kuma Garo da matsayin mataimakin takarar gwamna.
Garo dai shi ne ɗan taigigin farin kwamishinan Ganduje ɗin nan da aka nuno shi ‘yan Kwankwasiyya sun cire masa riga a Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, lokacin da aka Kama shi da mataimakin gwamna sun je wurin tattara ƙuri’u a Gama.
Gandujiyya na taƙama da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas, ɗan siyasar Kwankwasiyya, wanda ya koma Gandujiyya.
Abdullahi Abbas ɗan siyasa ne wanda tamkar mota ce wadda babu burki ta tunkari gungun jama’a gadan-gadan. To haka bakin Abdullahi Abbas ya ke, idan zai yi magana bai iya sa wa bakin sa linzami ba.
“Idan zaɓe ya zo kada Allah ya kiyaye.” Kaɗan kenan daga irin gunduma-gunduman maganganun da kan fito daga bakin sa. Da yawan wasu ma ba su buguwa a jarida saboda kaifin su. “Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai mun ci zaɓe.” Wasu kalaman na sa kenan.
To yanzu da aka yi gumurzun zaɓen shugaban ƙasa har Kwankwasiyya ta ta yi galaba kan Gandujiyya a zaɓen, shin ko Abba Gida-gida zai rama kayen da Ganduje ya yi masa a Gama, a zaɓen 2019?
Abubuwan da ke faruwa sun nuna tabbas Kwankwasiyya ta yi shiri sosai. Ta yi shirin yin ruwan ƙuri’u ga Abba Gida-gida. Kuma abubuwa da suka faru a lokacin kamfen da zaɓen shugaban ƙasa, ya nuna Kwankwasiyya ba za ta bari a sake yi mata “ko da tsiya-tsiya” ba.
Discussion about this post