A watan biyu na shekarar 2022, nayi rubutu makamancin haka mai taken “JIGAWA 2023: Wai Me Nene Zunubin Hadejia?”
Wannan rubutu ya dau hankalin duniya, harma wasu manyan jaridun wannan kasa sun wallafa shi, yana da ga cikin rubutun da ya dau hankali da tsokaci a shekarar da ta gabata. Nayi haka don hangen abin da ke faruwa a yau.
Ya kamata duk mai hankali ya tunawa kansa cewa, mu mutanen JIGAWA muna rayuwar mu cikin amana, mutunci da zaman lafiya. Wannan tun kafin gangar siyasa ta dau amo, haka kuma zamu ci gaba bayan gangar ta wuce.
Muna aiki tare, babu banbancin gari ko yanki, muna biyayya da junan mu, muna taimko ga junan mu, tun kafin gangar siyasa ta dau amo, haka kuma zamu ci gaba bayan gangar ta wuce.
Munyi auratayya a tsakanin mu, har mun hada dangi a junan mu. Wannan fa, tun kafin gangar siyasa ta dau amo, haka kuma zamu ci gaba bayan gangar ta wuce.
Duk wata magana ta gindaya kiyayya a tsakanin mu, akan siyasa ba alkhairi bane, kuma sharri zai koma kan mai yin sa.
Ya kamata mu kara tunatar da kawunan mu, cewa shi al’amuran mulki, bada mulki da hana mulki duk al’amuran Allah (SWA). Allah yana sha’anin sa yadda yaga dama ne, kuma in ya so yayi, duk shedanar Butulu ba ta hana Ubangiji tabbatar da ikon sa. A baya ma shi yaga dama, kuma wanda basu samu ba suka yi wa Allah shukura da karbar ikon sa.
Ya kamata mu sake hankalta da cewa, duk masu kirkirar karya da jingina ta ga wasu mutanen yankin wannan jiha tamu, ba sa zama a cikin mu, kawai yan ciranin siyasa ne, sun zo ne don biyan bukatar su ta kowana hali, sannan komai ya faru, su tafiya zasu yi, daman chiranin siyasa suka zo.
Saboda haka, babban muhimin abin da mutanen Jigawa zasu bawa muhimmanci shine, su zabi shugabannin su bisa chanchanta da fahimtar tsare tsaren da ‘yantakarar nan suke dashi da zai taimaki jihar Jigawa da kuma kawo mata cigaba.
Duk wani mai kokarin kawo wani batu don raba kawukan yan Jigawa to baya nufin alkhairi ga kowa, face hada husuma don biyan bukatar kawukan su.
Allah ya taima ki Jihar Jigawa.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post