Dan takarar gwamnan na jami’yyar PDP Isah Ashiru a ranar Talata ya samu karin karfin gwiwa a yunkurinsa na neman ɗarewa kujerar gwamnan jihar Kaduna yayin da jami’yyu 9 suka ce shi za su zaɓa a zaben wanda za a yi ranar 11 ga Maris.
Ashiru zai fafata ne da Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar.
Siyasa a jihar ta dauki wani gagarumin sauyin tun bayan zaben Shugaban kasa inda jami’yyar APC ta sha kasa a jihar sannan kuma ta rasa kujerun sanatoci biyu a majalisar dattawa da ta yi.
‘Yan takaran gwamnan daga jami’yyun daban-daban guda 9 sun ce sun janye daga takarar su za su mara wa Ashiru na PDP baya a zaben gwamna na da za ayi ranar 11 ga wata.
Jami’yyun da ke mara masa baya sun hada da; Young Progressives Party (YPP), African Alkiance (AA) , Allied People’s Movement (APM), All People’s Party (APP), All Progressives Grand Alliance (APGA), National Rescue Movement (NRM), Accord Party, Zenith Labour Party (ZLP) da Action Democratic Party, (ADP).
Jami’yyun dake karkashin kungiyar ‘ Kaduna State Rescue and Rebuild Gubernatorial Candidates Forum’ sun bayyana cewa ba su tare da takarar Muslim -muslim na APC.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Shugaban kungiyar Kuma dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jami’yyar YPP Sanin Yaya ya ce yarda su mara wa Ashiru baya ne saboda shine zai iya kawo ci gaba da hadin kan mutane a jihar.
Discussion about this post