Zababben gwamnan Kaduna Uba Sani Sanata Uba sani yayi alkawarin yin aiki tukuru a jihar Kaduna domin jin dadin mutanen jihar baki daya.
Sani ya bayyana haka a lokacin da ya ke amsar baƙuncin ƴan takara daga wasu jam’iyyun da suka fafata da shi a zaɓen 18 ga Maris a garin Kaduna.
Ƴan takarar sun ce sun zo ne domin su taya gwamna mai jiran gado murnar nasarar da ya samu da yi masa fatan alkhairi.
Da yake jawabi bayan ya saurare su gaba dayan su, sanata Uba Sani ya ce wannan ba nasara na ce na shi kaɗai nasara ce na kowa da kowa har da su da suka fafata da shi.
Daga nan sai yi alkawarin tafiya tare da kowa da kowa domin ci gaba mutanen jihar.
Bayan haka kuma ta amshi bakuncin kungiyar fastocin Kaduna da suma syka kawo masa ziyarar bangirma da murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan.
A karshe sanata Uba ya gide musu sannan ya yi fatan koma zai koma gida lafiya.
Discussion about this post