Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta gudanar da dukkan zaɓukan da ba su kammalu ba a ranar 15 ga Afrilu.
Zaɓukan sun haɗa da na wasu gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da na majalisar dokokin wasu jihohi.
Kwamishinan Wayar da Kan Jama’a kuma Babban Jami’in Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.
Ya ce hukumar ta sanar da hakan ne bayan ta cimma amincewa da yin zaɓukan a waccan ranar, kuma ta tattauna wuraren da za a yi zaɓukan a faɗin ƙasar nan, ko dai waɗanda aka jingine ko kuma wuraren da zaɓukan ba su kammalu ba.
Sanarwar ta zo ne mako ɗaya bayan an bayyana cewa zaɓukan gwamna a jihohin Kebbi da Adamawa duk ba su kammalu ba.
Wannan ne ya sa INEC ta bayyana sakamakon zaɓen jihohi 26, maimakon 28 da aka yi zaɓe a cikin su a ranar 18 ga Maris.
Za a yi zaɓen gwamna a Adamawa da Kebbi, sai kuma zaɓukan sanatoci a shiyyoyi biyar, ɗan majalisar wakilai ta ƙasa 31, mambobin majalisar dokokin jihohi 58.
“Mu na kira ga jam’iyyun, ‘yan takara da duk masu hannun a al’amurran da su ka shafi zaɓe, su lura da ranar da wuraren da za a yi zaɓen.
“INEC za ta yi amfani da ejan-ejan na rumfunan zaɓe da na cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe waɗanda ta rigaya ta tantance. Haka su ma masu sa-idon da aka rigaya aka tantance, ba a zai an ƙara tantance su ba, su da ‘yan jarida.
“Haka nan Hukumar Zaɓe na yin kira ga jam’iyyu da ‘yan takara da magoya bayan su, cewa su ɗauki zaɓe matsayin takara, ba yaƙi ba.
“Su guji furta kalaman da za su tunzura abokan adawa, tara mutane ba bisa ƙa’ida ba. Idan su ka kiyaye waɗannan, to za a gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali kamar yadda INEC ta tsara.”
Discussion about this post