Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi PDP cewa idan ta na da wani ƙorafi to ta garzaya kotu, amma ta daina ƙala wa Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Mahmood Yakubu sharrin da bai aikata ba.
INEC ta ce maganganun ɓata sunan da PDP ke yaɗawa kan Yakubu shugaban hukumar zai iya janyowa hukumar da kuma shugaban na ta su maka PDP kotu su nemi haƙƙin su.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban INEC mai suna Rotimi Oyekanmi ya yi wa PDP wannan gargaɗi, lokacin da ya ke amsa tambayoyi game da kiraye-kirayen neman Shugaban INEC ya sauka daga muƙamin sa.
Oyekanmi ya ce kiraye-kirayen PDP ta yi kwanan nan cewa Yakubu ya sauka kawai, bagararwa ce PDD ke yi kawai.
“Abin takaici kuma abin dubawa, duk da tulin da zargin da PDP ke wa Shugaban INEC, waɗanda dukkan su marasa tushe ne ballantana makama.
“Tabbas PDP ta kasa kawo ko da hujja guda ɗaya domin bai wa zargin da ta ke yi wata kariya cewa Yakubu ya aikata ba daidai ba ko ya karya dokar zaɓe ta 2022.
“Sannan kuma PDP ba ta bayar da hujjar cewa Yakubu ya yi maƙarƙashiyar ƙin loda sakamakon zaɓe daga na’urar BVAS ba.”
Oyekanmi ya ce abin takaici ne a surutan da PDP ta riƙa yi ba ta ce an yi maguɗi a dukkan sassan da PDP ɗin ta yi nasara a faɗin ƙasar nan ba.”
Kan haka ne INEC ta shawarci PDP idan ta na da wani ƙorafi a kan zaɓe, to garzaya kotu kawai.