Kungiyar manyan ma’aikatan Mai da Iskar Gas na kasa ya bayyana cewa lallai idan aka janye tallafin man fetur a ƙasar nan za arika siyan litar mai kan N450.
Festus Osifo, shugaban PENGASSAN ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) da aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Osifo ya yi magana ne kwanaki bayan ‘yan kasuwa da sauran kungiyoyi a sassan da ke karkashin masana’antar man fetur ta Najeriya sun ce cire tallafin zai sa farashin litar man fetur ɗaya ya koma Naira 750.
A watan Janairu, Ministar Kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed, ta ce zai fi dacewa gwamnati ta fara aiwatar da tsaretsarenta na tallafin man fetur a kashi na biyu na wannan shekara, musamman wanda ya shafe janye tallafin mai gaba daya.
A yau, Kamfanin Mai na Kasa wata NNPC ne kawai ya ke shigo da man fetur cikin kasar nan. Sannan kuma NNPC na samun canjin dala akan naira 400 zuwa 450 kowanne 1. Dubi da haka ya nuna ce za a rika saida litar mai daya akan N400.
PENGASSAN ya gargadi dillalan man fetur da su tabbata sun fito da mai su na siyar dashi, ” Duk dan kasuwan da muka samu yana harkallar boye mai za mu hukunta tashi.