Gwamnan Osun Ademola Adeleke ya gargadi bankunan jihar su daina biyan mutane tsoffin takardun kudi idan ba za su rika amsa ba idan aka dawo musu da shi ba.
Wannan gargadi na kunshe ne a cikin wata da kakakin gwamnan ya fitar ranar Litinin in da ya ce gwamnati ba za ta lamunci hakan da bankunan dake jihar ke yi ba.
” Ba za mu sa Ido mu bari bankuna na gasa wa mutanen mu aya a hannu ba. Su ne ke biyan su da tsoffin kudi, amma kuma idan suka dawo da kudin don a ajiye musu sai kuma su ki amsa. hakan ai rainin wayau.
Gwamnan ya kara da cewa hakan bai dace ba sannan ya yi kira ga babban bankin Najeriya ya gaggauta ba wa bankunan kasuwanci umarnin su ci gaba da amsar tsoffin takardun kudi.