Binciken da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo saboda halin rashin tabbas ɗin da Najeriya ta shiga, sakamakon mawuyacin ƙuncin rashin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Lamarin dai ya samo asali tun daga matsin da aka shiga sanadiyyar sauya launin kuɗi, inda Babban Bankin Najeriya, CBN ya tattara ilahirin kuɗaɗen da ke hannun jama’a da sunan sauya sabbin.
Sai dai kuma an shiga alaƙaƙai saboda har yau babu alamar samar da sabbin kuɗaɗen da za su wadaci bankuna, jama’a da sauransu domin sauƙaƙa hada-hadar yau da kullum.
Ƙaƙudubar tsadar rayuwa da hauhawar farashi na ci gaba da bibiyar Najeriya, baya ga dalilin canjin kuɗi akwai matsala ta ɗimbin bashin da ake bin Najeriya, wanda hakan ya hana tattalin arzikin ta hawa kan turba madaidaiciya.
A cikin watan Janairu, NBS ta tabbatar da cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 44.06.
Ga Bayanin Kamar Haka: Ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 44.06 – Hukumar Ƙididdiga:
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya a waje da cikin gida ya kai na naira tiriliyan 44.06.
Hukumar ta ce wannan adadin lissafin ƙarshen 2023, sai dai kuma na ta haɗa da naira tiriliyan 23 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin Najeriya ɗin ba.
Ƙididdigar ta tabbatar da cewa wannan bashi ya haɗa har na jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihar Legas ce ta ɗaya a jerin jihohin da su ka fi ciwo bashi, inda ake bin jihar bashin Naira biliyan 877. Sai jihar Delta da ake bin ta bashin naira biliyan 272..61, sai kuma ta uku Jihar Ogun da ake bi bashin naira bilyan 241.7.
Jihar Jigawa ce mafi ƙarancin kuɗaɗen da ake bi bashi na naira biliyan 44.
Wanda zai gaji Buhari zai gaji bashin naira tiriliyan 77 – Shugabar Ƙididdigar Bashi:
Babbar Daraktar Ofishin Tantance Adadin Basussuka ta Kasa (DMO), ta tabbatar da cewa gwamnati mai hawa a 2023 za ta gaji bashin naira tiriliyan 77.
Misis Oniha ta ce akwai bashin naira tiriliyan 44.06 da ake bin Najeriya a yanzu haka. To kuma idan aka haɗa da bashin naira tiriliyan 23 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin gwamnatin Buhari, adadin bashin zai tashi naira tiriliyan 77.06.
Oniha ta yi wannan bayani bayani dalla-dalla a ranar Alhamis, yayin da ake bai fi saura makonni bakwai a yi zaɓen Shugaban Ƙasa ba.
Buhari zai sauka a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
Makonni biyu da su ka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda CBN ya bai wa Gwamnatin Buhari bashin Naira tiriliyan 23.8 ba bisa ƙa’ida ba.
Zaune ta tashi tsaye a Majalisar Dattawan Najeriya, yayin da su ka gano cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa Gwamnatin Buhari ramcen tsabar kuɗi har naira tiriliyan 23.8 a cikin shekaru bakwai, ba bisa ƙa’ida ba.