Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta tara harajin Naira biliyan 487 a cikin watan Fabrairu.
Wannan adadin kuɗaɗen haraji ba su kai yawan Naira biliyan 653.704 da aka tara watan Janairu ba.
Adadin harajin da aka tara a watan Janairu ya haura na Fabrairu da Naira biliyan 166.598.
Harajin dai an tara Naira biliyan 224 daga Harajin Jiki Magayi, wato ‘VAT’.
Sai kuma Naira biliyan 11.645 da aka tara matsayin harajin da gwamnatin tarayya ke tatsa da duk wanda ya yi taransifa ɗin kuɗi ta Na’urori, wato EMTL.
Wanan sanarwar na ƙunshe ne a cikin bayanan da Kwamitin Rarraba Kuɗaɗen Shiga Ga Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi ya fitar na watan Maris.
Sanarwar ta ce Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi sun raba Naira biliyan 772 a tsakanin su cikin watan Fabrairu.
Haka kuma sanarwar ta ce sauran kuɗaɗen da su ka rage a Asusun Rarar Ribar Fetur (ECA) a wancan watan, dala 474,754.57 ne kacal.
An bai wa Gwamnatin Tarayya Naira biliyan 267, an raba wa jihohi jimillar Naira biliyan 236 baki ɗayan su, sai kuma ƙananan hukumomi da aka bai wa biliyan 173.936.
Su kuma jihohi masu arziki ɗanyen man fetur, an raba masu naira biliyan 43.