Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tatsi harajin ‘VAT’ na Naira biliyan 697 tsakanin Satumba zuwa Disamba, 2022.
NBS ta bayyana haka a ciki rahoton ta mai ɗauke da ƙididdigar kuɗaɗen harajin ‘VAT’ na watanni huɗun ƙarshen shekarar 2022.
A cikin rahoton wanda ta fitar a ranar Laraba, NBS ta ce an samun ƙarin kuɗi har kashi 11.51, idan aka kwatanta da Naira biliyan 625.39 da aka tara na harajin ‘VAT’ tsakanin Mayu zuwa Agustan 2022, wato watanni huɗu kafin watanni huɗun ƙarshen shekara.
NBS ta ci gaba da cewa daga cikin naira biliyan 697 ɗin da aka tara, an tatsi Naira biliyan 408.12 a harajin ciki gida na VAT, sauran naira biliyan 159.83 kuma daga harajin VAT na waje aka tara su. Sai cikon naira biliyan 129.43 daga ‘VAT’ ɗin kayan da shigo da su daga waje.
A ƙididdigar, fannin noma, gandun daji da kiwon kifi ne koma-baya wajen tara kuɗaɗen haraji.
NBS ta ce kuɗaɗen da aka tara a watanni huɗun ƙarshen 2022, sun fi na watanni huɗun ƙarshen 2021 yawa da kashi 23.71.