Akwai mata 24 da za a fafata zaɓen gwamna da su a wasu jihohin ƙasar nan, a ranar Asabar mai zuwa.
Sai dai kuma biyu kaɗai su ka fito takarar a cikin manyan jam’iyyun ƙasar nan guda uku, wato APC, PDP da kuma LP.
Sauran mata 22 kuma duk sun fito ne a ƙananan jam’iyyu daban daban.
AISHATU BINANI: Aishatu Binani ita ce ta ci zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a Jihar Adamawa a ƙarƙashin APC. Cikakken sunan ta Aishatu Ɗahiru, amma an fi sanin ta da Binani. Mace ce mai zurfin ilmi, wadda ta yi karatu a Ingila.
Ana ganin za ta yi gwagwagwa da Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP, wasu ma na ganin tuni za ta kayar da shi tun kafin La’asar sakaliya.
Aishatu tun a zaɓen fidda gwani na nuna babu wani namiji da zai ba ta tsoro, ta kayar da irin su tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu.
Ƙalubale Da Shingayen Da Ke Gaban Binani:
Bayan Binani ta yi nasara a kotu, babban abin da kuma ke gaban ta a yanzu shi ne yadda wasu malaman addini a Arewacin Najeriya ke ta hayaƙin tayar da jijiyoyin wuyan kamfen ɗin kada a zabi mace ta shugabanci jihar Adamawa.
Masu nuni da haramcin haka na cewa idan mace ta zama shugaba, to dukkan limamai da malaman addinin musulunci da Sarakuna ma sun koma a ƙarƙashin mace.
Sai dai kuma malamai da sauran musulmai masu goyon bayan ta, su na kafa hujja da cewa ai tun farko ma tunda dai kwansitushin ba mulkin tsarin musulunci ba ne, babu wani bambanci tsakanin shugabancin mace ko namiji. Domin wanda ba Musulmi ba ma ya na shugabanci a ƙasar nan. Don haka babu wani tawilin da malami zai yi ya hana su zaɓen Binani a tsarin dimokraɗiyya, wanda ba na Musulunci ba.
A jihar Abiya akwai wata mace mai himma wato Gladys Johnson-Ogbuneke wadda ta fito a ƙarƙashin SDP da kuma Lancaster Okoto wadda ke takarar ta a PRP.
A Jihar Akwa Ibom akwai Ekanem Abesiekeme ta AAP da kuma Udoh Emem Monday ta SDP.
Jihar Benuwai akwai mata biyu, Roseline Chenge ta ADP da kuma Aondona Dabo-Adzuana ta ZLP.
A Jihar Barno wata mai suna Fatima Abubakar ta fito wa ADP, sai kuma wata a jihar Cross River mai suna Ibiang Marikana Stanley, ita ma a ADP.
A Jihar Delta ma akwai mata biyu, ɗaya mai suna Onokiti Helen da Cosmos Annabel, su biyun a ƙarƙashin APP.
A Jihar Ebonyi akwai Chinenye Igwe ta APM sai kuma a jihar Enugu akwai Ogochukwu Nweze, ta SDP.
A Jigawa Binta Umar Yahaya ta jam’iyyar AA, sai Kano mai mata biyu, Furera Ahmad Yakubu BP, Aisha Mahmud NRM.
Jihohin Kwara da Legas da Nasarawa da Neja da Oyo duk akwai mata masu takarar gwamna. Haka jihar Ribas da Zamfara Hadiza Usman ‘yar takarar gwamna ta ZLP a jihar Zamfara.