Gwamnatin jihohin PDP bakwai sun janye ƙarar da su ka maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Ƙoli, wadda su ka shigar bisa ƙin amincewa da yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya da ta Dattawa.
Sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen da kuma tsarin da INEC ta bi wajen tattara sakamakon zaɓen.
Sanarwar janye ƙarar na ƙunshe ne cikin bayanin da lauyan gwamnatocin bakwai, wato Mike Ozekhome ya fitar a ranar Juma’a, ya aika wa kotun a madadin waɗanda ya ke wakilta.
Sun shigar da ƙarar bisa zargin cewa INEC ta karya ƙa’ida, domin ba ta aika da saƙo a manhaja kamar yadda doka ta tanadar ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamnatin jihohin PDP shiga su ka garzaya Kotun Ƙoli, su ka ce sun ƙi amincewa da nasarar Bola Tinubu.
Gwamnatin jihohi shida na PDP sun garzaya Kotun Ƙoli, inda su ka ƙalubalanci zaɓen Shugaban Ƙasa da kuma na Majalisar Dattawa da na Tarayya.
Gwamnatocin jihohin shida sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da kuma Sokoto.
Antoni Janar-janar kuma Kwamishinonin Shari’a na jihohin ne su ka shigar da ƙarar, su na neman Kotun Ƙoli ta shiga batun zaɓen baya-bayan nan da aka kammala, domin kauce wa ɓarkewar rikici.
Jihohin shida waɗanda dukkan su jihohin PDP ne, su na nuna rashin amincewa da nasarar da INEC ta ce Bola Tinubu na APC ne ya lashe zaɓen 2023.
A cikin ƙarar da suka shigar, sun bayyana cewa ba a bi ƙasar Dokar Zaɓe ba kafin a bayyana cewa Bola Tinubu ne ya yi nasara.
Musamman gwamnatocin na jihohi shida su na ƙalubalantar rashin loda sakamakon zaɓe a manhajar iRev ta hanyar yin amfani da na’urar tantance masu rajista, wato BVAS.
Sun ce Gwamnonin waɗannan jihohi shida su na da haƙƙin bin hanyoyin da su ka dace domin gudun kada hargitsi ya tashi a jihohin su.
Sun dai shigar da ƙarar tun a ranar 28 ga Fabrairu, kafin a bayyana sunan wanda ya yi nasara.