Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya bayyana cewa Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami sun yaudari Shugaba Muhammadu Buhari, su ka ba shi gurguwar shawarar sauya launin kuɗi, har ta kai tsarin ya gurgunta ‘yan Najeriya da ƙasar baki ɗaya.
“Tun da a yanzu Kotun Ƙoli ta bayar da umarni a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗaɗe har zuwa ranar 31 Ga Disamba, ya zama wajibin CBN da Godwin Emefiele su naɗe tabarmar kunya, su fito wa jama’a da kuɗaɗen su, sabbi da tsoffin a ci gaba da amfani da su.”
Akeredolu kuma ya ce tunda Kotun Ƙoli ta haramta taƙaita cirar kuɗaɗe zuwa naira 20,000 ko Naira 2,000 a rana ɗaya, dole CBN ya bi doka, ya sakar wa jama’a kuɗaɗen su a riƙa cirewa ta ATM.
“Gwamnan CBN da Ministan Shari’a sun yaudari Shugaba Muhammadu Buhari, sun maida shi kamar wani Fir’aunan da ya fi ƙarfin dokar ƙasa, shi kuma Buhari ya ɗauki rigar Fir’aunancin ya rataya a wuya, an ƙaƙaba wa jama’a ƙuncin rayuwa na babu gaira, babu dalili.
“Miliyoyin jama’a sun shiga ƙaƙanikayi, wasu miliyoyin sun rasa sana’o’in su, jarin wasu miliyoyin ya karye. Wasu sun mutu wurin canjin kuɗi, wasu kuma takaici ya sa sun yi tsirara cikin bankuna, saboda an riƙe masu kuɗaɗe, ba su iya cira su ciyar da iyalan su.”
Idan ba a manta ba, kafin zaɓen Shugaban Ƙasa sai da Akeredolu ya ce an ƙirƙiro canjin kuɗi ne don kawai a goga wa gwamnatin APC baƙin jini.