Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sake yin kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara cewa su ɗauki zaɓen ranar Asabar a matsayin gasa ko kuma takara, amma ba yaƙi ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan kira da kuma gargaɗi, lokacin da ya ke jawabi wurin kwamitin hukumomi masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da zaɓe.
A wurin taron wanda aka yi ranar Talata a Abuja, Yakubu ya yi kira ga jam’iyyu su guji aikata duk wani abin da zai iya kawo wa zaɓe cikas.
Kuma ya roƙe su kada su riƙa zagayawa su na ƙoƙarin haɗa baki da jami’an INEC, ko kuma yin abin da zai iya kawo wa rayukan jami’an zaɓe da na masu sa-ido barazana.
Ya ce zaɓen gwamna wanda za a yi a ranar Asabar, za a yi ne a jihohi 28, banda jihohin Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Ondo da kuma Osun.
Shugaban na INEC ya ƙara da cewa za a yi zaɓukan majalisar jihohi a dukkan mazaɓu 993 na faɗin ƙasar nan.
“Ba kamar zaɓe ranar 25 ga Fabrairu ba, wanda ya gudana a mazaɓu 470 kaɗai da suka ƙunshi na shugaban ƙasa ɗaya, na Majalisar Dattawa 109 sai na Majalisar 360. Shi wannan zaɓe na Jiha, za a yi ne a mazaɓu 1,021, da su ka ƙunshi gwamnoni 28, sai ‘yan majalisar dokoki 993.
“Sannan kuma za a samu yawan sunayen ‘yan takara a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe da kuma yawan ejan-ejan masu kare ƙuri’un su.
“Saboda haka ya na da kyau jam’iyyu su sanar da ejan-ejan ɗin su su kiyaye aikata dukkan abin da zai kawo cikas, su kuma tuna cewa shi da zaɓe takara ce, ba yaƙi ba ne.”
Da ya ke jawabi, Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Fannin Tsaro, Manjo Janar mai ritaya Babagana Monguno, ya shawarci ‘yan siyasa su ja wa magoya bayan su kunne, domin a tabbatar an samu gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a ranar Asabar.
Ya ce duk wani taƙadarin da ke shirin kawo cikas ga zaɓen ranar Asabar, to ya canja tunani, ko kuma ya haɗu da fushin hukuma.
Discussion about this post