Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya bayyana cewa ya na jagorancin gangamin kayar da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ne, kuma tuni Bala ya ɗanɗana kaifin makaman da su Dogara ɗin su ka fafata yaƙi da shi.
Dogara ya yi wannan bugun ƙirjin a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV ta yi da shi a ranar Laraba, inda ya ce gwamna ne za a ci ya rasa zaune, ya rasa tsaye a siyasar jihar, ba shi Dogara ba.
Tsohon Kakakin Majalisar dai da wasu jiga-jigan PDP a Bauchi, ciki har da Bello Kirfi, wanda tsohon Minista ne, da tsohon Gwamna Isa Yuguda, da tsohon Sanata Nazifi Sulaiman, su na goyon bayan ɗan takarar APC, Saidique Abubakar ne. Ba su goyon bayan Gwamna Bala, ɗan takarar jam’iyyar su.
Dogara ya ce shi fa bai fita daga PDP ba, kuma bai shiga APC ba, amma dai ya na jagorantar rundunar yaƙin tabbatar da cewa Sadique ɗan takarar APC ya yi nasarar lashe zaɓen gwamnan Bauchi.
Ya ce zaratan mayaƙan sun kafsa da runduna Gwamna Bala, kuma gwamnan ya gane cewa sun fi ƙarfin sa, sun kuma sun fi shi yawan jama’a.
“Gwamna ya fito ya ce yaƙi ne tsakani na da shi kan sa. To an yi zaɓe kuma ɗan takara ta shi ne ya yi nasara.
Ya tsayar da ɗan takarar da zai ƙwace kujera ta a Majalisar Tarayya. Ni kuma na tsayar da nawa ɗan takarar a APC. Kuma mu ka kayar da ɗan takarar da na tsayar ya kayar da na sa ɗan takarar.
“Sannan abin kunya ɗan majalisar tarayya daga Ƙaramar Hukumar Alƙaleri da Kirfi ma ɗan APC ne, na sa ɗan takarar ya sha kaye.” Haka Sanatan Shiyyar gwamna shi ma wanda aka zaɓa a 2023 ɗan APC ne.”
Dogara da Kirfi dai manyan ‘yan PDP ne. Sun matsala da Gwamna Bala, wadda hakan ya haifar da su ka goya wa APC baya a zaɓen shugaban ƙasa da ma majalisar tarayya. Yanzu kuma sun sha alwashin sake goya wa ɗan takarar APC baya a zaɓen gwamna, domin su hana Bala yin zango na biyu.
Discussion about this post