Jawabin karɓar nasarar zaɓen shugaban ƙasa, daga Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Najeriya,
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,
Jinjina ga ‘yan Najeriya,
Ina mai matuƙar jinjina da miƙa wuya gare ku, tare da alfahari da yadda ku ka zaɓe ni, a matsayin shugaban ƙasa na 16 na Najeriya. Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwar ko ma wane mutum ne, kuma tabbaci ne na ɗorewa da wanzuwar dimokraɗiyyar mu. Ina ƙara yi maku godiya daga zuciya ta.
Magoya Bayan Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso Sun Cancanci Yabo:
Ko kai mai goyon bayan Tinubu ne, ko Atiku, ko Obi, ko ɗan Kwankwasiyya, kai ko ma wace jam’iyya ka ke goyon baya, zaɓen da ka yi zaɓe ne na neman ingantacciyar ƙasa, wadda ka ke fatan wanzuwar ɗorewar ta. Ina gode maku da rawar da ku ka taka wajen jajircewar ku ga dimokraɗiyyar mu.
Kun amince kun miƙa yaƙinin ku da amanar ku ga dimokraɗiyyar Najeriya, bisa ginshiƙin ɗorewar haɗin kai, gaskiya, zaman lumana da kuma yarda da juna. Yanzu fata na gari kowa ke wa Najeriya, kuma fata na gari ta wanzu a Najeriya kenan. Dama kuma fata na gari, ai lamiri ce.
Godiya Ga INEC Ta Gudanar Da Sahihin Zaɓe:
Mu na godiya ga INEC da ta gudanar da sahihin zaɓe. Ɗan cikas ɗin da aka samu kaɗan ne, kuma bai yi wani tasiri wajen fitar da wanda ya yi nasara ba. Amma duk lokacin da zaɓe ya zo, mu na ƙara inganta tsarin domin yin karsashi sosai a dimokraɗiyyar mu.
A yau Najeriya ta ƙara zama uwa a Nahiyar Afirka. Hasken ta ya fi annuri a matsayin ta na ƙasar dimokraɗiyya mafi girma a Afrika.
Ina miƙa godiya ta ga dukkan waɗanda su ka taya ni kamfen. Tun daga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya jagoranci rundunar yaƙin neman zaɓe, zuwa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Gwamnonin APC Gaishe Ku Da Gwagwarmaya:
Ku kuma Gwamnonin APC da sauran shugabannin jam’iyya da sauran magoya bayan APC duk ku na bi na bashin godiya. Na gode ƙwarai. Kuma ina godiya ga ɗaukacin rundunar yaƙin neman zaɓe.
Ina godiya ga mata ta da iyali na, waɗanda ba don gudummawar ku ba, wannan nasara da ba ta samu ba.
Ina godiya ga Allah (SWT) da ya ba ni nasara a wannan zaɓen. Allah ka ba ni ƙarfin ɗaukar wannan nauyin shugabanci. Domin shi ne ya ƙaddara za ni zama shugaban ƙasa.
Daga ƙarshe, ina godiya ga dukkan ‘yan Najeriya bisa ga bin doka da odar su kan tafarkin dimokraɗiyya. Zan yi maku adalci, na zan ba ku kunya ba wajen ganin mun samar da ƙasar da za mu ci gaba da yin alfahari da ita.
Atiku, Kwankwaso Da Obi ‘Yan’uwa Na Ne, Ba Abokan Gaba Na Ba:
Ina kira ga sauran ‘yan takara, tun daga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku, tsohon Gwamna Kwankwaso, tsohon Gwamna Obi da sauran ‘yan takara, ina miƙo maku goron gayyatar danƙon zumunci a cikin amana da gaskiya.
Yanzu tilas mu watsar da siyasar takara mu rungumi tafiya tare mu tsira tare.
A lokacin kamfen dukkan ku abokan adawa ta ne. Amma fa ba ku taɓa zama abokan gaba na ba. Har a cikin zuciya ta ku ‘yan’uwa na ne.
Wanda Bai Gamsu Da Zaɓe Ba Ya Tafi Kotu, Kada Ya Hau Kan Titi:
Duk da haka na san wasu ‘yan takarar zai yi wahala su amince da sakamakon zaɓen. Ku na da ‘yancin neman haƙƙin ku a kotu. Abin da kawai bai dace ba shi ne mutum ya ɗauki doka a hannun sa. A kotu za a ƙalubalanci sakamakon zaɓe, ba a kan titi ba.
Ina kira ga magoya baya na kada su ruruta tashin hankali.
Ya kamata duk wanda sakamakon zaɓen nan bai yi masa daɗi ba, ya kai zuciya nesa. Ku zo mu tafi tare.
Matasan Najeriya Kun Samu Abin Da Ku Ke So:
Na dawo kan ku matasan Najeriya, na fahimci abin da ke maku zafi a cikin zukatan ku. Ku na neman nagartacciyar gwamnati, ingantaccen tattalin arziki da ƙasa mai zaman lafiya, wadda za ta kare ku ta kare wanzuwar ku nan gaba.
Ina Tutiya Da Basirar Kashim Shettima:
Mataimakin takara ta kuma Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, na fahimci kalubalen da ke kan mu. Ni kuma musamman na san irin ƙwazo da basirar da ka ke da ita. Na san ni da kai za mu gina nagartacciyar Najeriya.
Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya za mu haɗu baki ɗayan mu mu gina ƙasaitacciyar Najeriya, wadda kowa zai riƙa tutiya da bugun-ƙirji cewa shi ɗan Najeriya ne.
Ina godiya gare ku baki ɗaya.
Allah ya albarkace ku.
Allah ya albarkaci Najeriya.