Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya nuna sha’awar zama shugaban majalisar dattawa to 10.
Ya ce idan dai aka yi adalci har aka bai wa yankin Kudu maso Gabas muƙamin,to shi ne ya fi kowa cancanta ya riƙe muƙamin a jerin dukkan sanatocin APC na yankin.
Kalu ya bayyana haka ranar Talata, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
Za a rantsar da ‘Yan Majalisa ta 10 a cikin watan Yuni.
“Zan so a ce APC ta miƙa muƙamin Shugaban Majalisar Dattawa ga yanki na, a yankin nawa kuma a ƙauye na Igbere, saboda Shugaban Ƙasa mai jiran gado na buƙatar nagartattun mutanen da za su taimaka masa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma taimakawa wajen kafa dokokin da shugaban zai ji sauƙin amfani da dokoki wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
“Saboda ni masanin tattalin arziki ne, kuma ɗan kasuwa.” Inji Kalu.
Tsohon gwamnan na Jihar Abiya ce shi ne ya fi dukkan sauran sanatocin Kudu maso Gabas cancanta idan aka yi la’akari da ƙa’idojin da Majalisar Dattawa ta shimfiɗa.
“Idan mu ka yi la’akari da ƙaidojin Majalisar Dattawa, kuma idan har dimokraɗiyyar gaskiya ake yi a ƙasar nan, to na ma fi ƙarfin yin takarar wannan matsayi da kowa, saboda a Majalisar Dattawa ni ne na huɗu bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Mataimakin Shugaba da Shugaban Masu Rinjaye a yanzu haka da mu ke kan mulki a yanzu na Majalisar Dattawa ta 9.
“Saboda haka ba ma zai yiwu ba a miƙa muƙamin Shugaban Majalisar Dattawa ga sabon-shigar majalisa.
Kalu ya jinjina wa INEC dangane da ƙoƙarin da ya ce ta yi wajen gudanar da zaɓen 2023. Sai dai kuma ya ce a duk duniya babu inda ake yin zaɓe ya tafi 100 bisa 100 babu tawa tangarɗa ko kaɗan.
Discussion about this post