Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya roki mutanen jihar Kaduna su yafe masa kurakuran da yayi a jihar a tsawon lokacin da yake gwamna.
A taron gungun magoya bayan jam’iyyar da yayi a jihar Kaduna tare da ɗan takarar gwamnan jihar Sanata Uba Sani.
Gwamnan ya ce sanata Uba sani ne zai ci gaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ta ɗauko ta saka a gaba. ” Amma idan kuka zaɓi wasu da ba ƴan jam’iyyar ba za su zo da sabbin abubuwa da zasu ruguza abubuwan da muka yi a baya.
“Idan an yi ma wani laifi ya yi hakuri. Kada laifina ya shafi Sanata Uba Sani da Dakta Hadiza”
“Ina rokon ku goyon bayan da kuka ba ni ku ninka ku ba Sanata Uba Sani da Dakta Hadiza saboda su ci gaba da ayyukan da muka fara na alheri, sannan su gyara inda muka yi kura-kurai”
Tun a lokacin da gwamna El-Rufai ke magana, da yawa cikin mutanen da ke cikin wannan ɗakun taro suka rika ɗirka kowar sun ya fe masa.
Za a gudanar da zaɓen gwamna da na majalisun jiha ranar 11 ga wata a faɗin ƙasar nan.
A jihar Kaduna sanata Uba Sani na APC zai fafata ne da Isah Ashiru na PDP, Suleiman Hunkuyi ma NNPP sai kuma Hayatuddeen na PRP da Jonathan Asake na LP.
Discussion about this post