Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Sokoto, Nura Ali.
Sakatariyar INEC Rose Orlaran-Anrhony ce ta yi sanarwar dakatarwar a cikin wata takarar manema labarai.
Ta bayyana sunan Hajiya Aliyu Kangiwa matsayin sabuwar Kwamishinar Zaɓe ta Jihar Sokoto.
Haka nan INEC ta yi wa Ali kakkausan gargaɗin cewa kada ya kuskura ko hanya ta bi da shi ta kusa da Ofishin INEC na Sokoto, har sai ya ji wani umarni daga sama.
“Wannan sanarwa ce gare ka, cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da kai, kuma ta na gargaɗin ka nesanci kusa da Ofishin INEC na Sokoto, har sai yadda hali ya yi tukunna.”
“An umarci Sakatariyar Gudanarwar Ofishin INEC ta Sokoto ta karɓi ikon riƙe Ofishin INEC ɗin daga hannun ka, yanzu-yanzu.
Yayin da INEC ba ta bayyana dalili ba, majiyoyi daban-daban sun ce dakatar da Ali ba ya rasa nasaba da zargin tafka rashin gaskiya da rashin adalcin da ake cewa ya yi a zaɓen shugaban ƙasa a jihar Sokoto.
A wani labarin kuma, INEC ta nemi kotu iznin yi wa na’urorin BVAS garambawul kafin zaɓen gwamnoni.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta garzaya Kotun Ɗauka Ƙara domin neman iznin yi wa na’urorin tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) garambawul, kafin zaɓen ranar 11 ga Maris.
Za a yi zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki jihohi a ranar Asabar, 11 ga Maris.
INEC ta garzaya kotun ne kwana biyu bayan kotu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP iznin binciken na’urorin BVAS waɗanda aka yi zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya da su.
Sun nemi iznin ne domin su ƙara kafa wa kotun hujjojin da su ke dogaro da su dangane da zargin maguɗin da su ke cewa an yi a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu.
Sai dai kuma INEC ta je Kotun Ɗaukaka Ƙara ta na neman a ɗage mata hukuncin hana ta taɓa na’urorin BVAS bayan zaɓen shugaban ƙasa.
Kotun ta hana INEC taɓa su ne, saboda ta bai wa PDP da LP iznin binciken na’urorin domin su gano zargin maguɗin da su ke iƙirarin an yi, idan har an yi ɗin.
Sai dai kuma kwanaki biyu bayan an bai wa su Atiku iznin binciken BVAS, ita ma INEC ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta nemi iznin cewa a ba ta damar yi wa na’urorin garambawul saboda da su ne za ta yi aikin tantance masu zaɓen ranar 11 ga Maris.
INEC ta ce idan ba ta yi masu garambawul ɗin ba da wuri saboda an ce ta nesance su, tunda an bai wa Atiku da Obi iznin binciken su, to sai dai fa idan ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki za ta yi.
Ta kafa hujjar cewa ba a Abuja ake aikin yi wa na’urorin garambawul ba, kuma aikin ya na ɗaukar lokaci.