Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) ta yi kintacen cewa aƙalla mutum miliyan 25.3 ne za su galabaita a Najeriya sanadiyyar matsalar karanci da rashin sukunin samun abinci tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta, 2023.
Rahoton duk bayan wata uku da FAO ta fitar baya bayan nan, ya nuna cewa adadin waɗanda yunwar za ta kassara sun wuce mutum miliyan 19.5 ɗin da su ka galabaita a shekarar 2022.
Ki
Rahoton FAO dai ya yi bincike da nazarin ƙasashe 45 domin bibiyar abin da ka je ya dawo ta ɓangaren abinci, tare da musamman ma a ƙasashen da ke fama da matsalar rashin samun kuɗin shiga a fannonin noma.
Rahoton ya ƙara da yin nunin cewa matsalar rashin tsaro ta taimaka sosai wajen ruruta ƙarancin abinci da kuma yunwa a cikin Najeriya.
“Matsalar ƙarancin abinci ta yi muni sosai saboda matsalar rashin tsaro a yankin Arewa, wanda ya zuwa watan Maris 2022, waɗanda su ka tsere bayan sun rasa muhallin su har mutum miliyan 3.17.
“Yawanci waɗannan mutum miliyan 3.17 kuwa idan aka yi duba za a fahimci cewa duk mutanen karkara ne, waɗanda sai da noma za su iya samun abinci.
Rahoton ya ce ‘yan bindiga sun hana manoma fita gona, hakan kuwa ya janyo gagarimar matsalar ƙarancin abinci.
Ciki makon jiya ma Hukumar Ƙididdigar Alƙaluma ta Kasa (NBS ta ce hauhawar farashi da tsadar rayuwa na ci gaba da kwankwatsar talakawa, saboda ƙarancin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Binciken da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo saboda halin rashin tabbas ɗin da Najeriya ta shiga, sakamakon mawuyacin ƙuncin rashin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Lamarin dai ya samo asali tun daga matsin da aka shiga sanadiyyar sauya launin kuɗi, inda Babban Bankin Najeriya, CBN ya tattara ilahirin kuɗaɗen da ke hannun jama’a da sunan sauya sabbin.
Sai dai kuma an shiga alaƙaƙai saboda har yau babu alamar samar da sabbin kuɗaɗen da za su wadaci bankuna, jama’a da sauransu domin sauƙaƙa hada-hadar yau da kullum.
Ƙaƙudubar tsadar rayuwa da hauhawar farashi na ci gaba da bibiyar Najeriya, baya ga dalilin canjin kuɗi akwai matsala ta ɗimbin bashin da ake bin Najeriya, wanda hakan ya hana tattalin arzikin ta hawa kan turba madaidaiciya.
A cikin watan Janairu, NBS ta tabbatar da cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 44.06.
Ga Bayanin Kamar Haka: Ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 44.06 – Hukumar Ƙididdiga:
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya a waje da cikin gida ya kai na naira tiriliyan 44.06.
Hukumar ta ce wannan adadin lissafin ƙarshen 2023, sai dai kuma na ta haɗa da naira tiriliyan 23 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin Najeriya ɗin ba.
Ƙididdigar ta tabbatar da cewa wannan bashi ya haɗa har na jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihar Legas ce ta ɗaya a jerin jihohin da su ka fi ciwo bashi, inda ake bin jihar bashin Naira biliyan 877. Sai jihar Delta da ake bin ta bashin naira biliyan 272..61, sai kuma ta uku Jihar Ogun da ake bi bashin naira bilyan 241.7.
Jihar Jigawa ce mafi ƙarancin kuɗaɗen da ake bi bashi na naira biliyan 44.
Wanda zai gaji Buhari zai gaji bashin naira tiriliyan 77 – Shugabar Ƙididdigar Bashi:
Babbar Daraktar Ofishin Tantance Adadin Basussuka ta Kasa (DMO), ta tabbatar da cewa gwamnati mai hawa a 2023 za ta gaji bashin naira tiriliyan 77.
Misis Oniha ta ce akwai bashin naira tiriliyan 44.06 da ake bin Najeriya a yanzu haka. To kuma idan aka haɗa da bashin naira tiriliyan 23 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin gwamnatin Buhari, adadin bashin zai tashi naira tiriliyan 77.06.
Oniha ta yi wannan bayani bayani dalla-dalla a ranar Alhamis, yayin da ake bai fi saura makonni bakwai a yi zaɓen Shugaban Ƙasa ba.
Buhari zai sauka a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
Makonni biyu da su ka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda CBN ya bai wa Gwamnatin Buhari bashin Naira tiriliyan 23.8 ba bisa ƙa’ida ba.
Zaune ta tashi tsaye a Majalisar Dattawan Najeriya, yayin da su ka gano cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa Gwamnatin Buhari ramcen tsabar kuɗi har naira tiriliyan 23.8 a cikin shekaru bakwai, ba bisa ƙa’ida ba.
Yadda Aka Bankaɗo Rufa-rufar:
A ranar Laraba ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙarin neman amincewar Majalisar Dattawa ta sa hannu cewa ta amince CBN ta bayar da bashin, wanda an rigaya an karɓa, har an dagargaje kuɗaɗen. Shi ne maimakon gwamnatin Buhari ta nemi amincewar Majalisar Dattawa, sai yanzu ta nema a makare, bayan an karɓa, an kashe tuni.
Na farko dai gwamnatin Buhari ki kuma a ce Shugaba Buhari ya karya doka, saboda ya yi ta karɓar kuɗaɗen daga CBN ba tare da neman amincewar Majalisar Dattawa ba.
Na biyu, CBN da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun karya doka, domin sun bai wa Gwamantin Buahri bashin da ya wuce ƙa’idar da ya kamata a bayar har sau 2900%.
Adadin Nawa Dokar Najeriya Ta Ce CBN Ya Ramta Wa Gwamnatin Tarayya?:
Dokar CBN ta cikin Kundin Dokokin Najeriya ta ce, “idan gwamnatin tarayya na fama da giɓin kasafin kuɗaɗe, za ta iya ramcen kuɗi daga CBN. Amma adadin da CBN zai bayar kada ya wuce kashi 5% kacal na jimlar kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar da ta gabata.”
Illar Wannan Bashin Rufa-rufa:
Wannan bashi a gwamnatin Buhari ta ci daga CBN ba bisa ƙa’ida ba, ya karya doka, ya haifar da tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa, hauhawar farashi, gurguncewar tattalin arziki da kuma jibga ɗimbin bashi a wuyan kowane ɗan Najeriya, har waɗanda za a haifa nan da shekaru masu zuwa.
Bashin Nawa Buhari Ya Gada Daga CBN:
Lokacin da Buhari ya hau mulki a Mayu, 2015, ya taras da bashin naira biliyan 789.7 da gwamnatin baya ta ciwo daga CBN.
Amma tsakanin Janairu zuwa Oktoba 2022, kaɗai a wannan shekarar, Gwamnatin Buhari ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.6 daga CBN.
Tsakanin 2012 zuwa Mayu, 2015 kafin hawan Buhari, CBN na bin gwamnatin tarayya bashi na naira biliyan 654.9 kacal.
Ƙa’idar Karɓar Bashin CBN:
Dokar Najeriya cewa ta yi, “Gwamnatin Tarayya ta riƙa gaggauta biyan bashin da ta karɓa kafin ƙarshen shekarar
da ta karɓi bashin. Ko kuma kafin sake karɓar wani sabon bashin.”
Sai dai kuma duk Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Ahmed sun sa ƙafa sun take wannan doka.
A Ƙa’ida, Bashin Naira Biliyan 219 Ya Kamata CBN Ya Ba Gwamantin Buhari A 2022, Ba Naira Tiriliyan 5 Ba:
Saboda naira biliyan 219 su ne kashi 5% na adadin kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar 2021.
Yadda Gwamnatin Buhari Ta Riƙa Karɓar Bashin CBN:
CIkin 2017 har bashin da CBN ke bi ya kai naira tiriliyan 3.3.
Zuwa Disamba 2018 kuma bashin ya kai Naira tiriliyan 5.4, zuwa Disamba 2019 kuwa ya kai naira tiriliyan 8.7.
Zuwa Disamba 2020 bashin ya cilla sama har zuwa
naira tiriliyan 13.1. Zuwa Disamba 2021 ya kai Naira tiriliyan 17.4.
Yanzu kuwa zuwa Disamba 2022, bashin ya kai naira tiriliyan 23.8, kuma ko sisi gwamnati ba ta taɓa ko fara biya ba.
Bashin Da Ko Gwamnatin Jikokin Mu Ba Za Su Iya Biya Ba:
Cikin watan Oktoba 2022 ne Gwamnatin Tarayya ta rattaba cewa sai nan da shekaru 40 za a kammala biyan bashin, a kan kuɗin ruwa na kashi 9%. Kenan babu ruwan gwamnatin Buhari ya jeƙala-jeƙalar biyan bashin.
Tuni dai Majalisar Dattawa ta ce a binciki ayyukan da aka ce an yi da kuɗin.
A gefe ɗaya kuwa masu sharhi na cewa hatta sabbin kuɗaɗen da CBN ya buga, duk wata rufa-rufa ce kawai.
Discussion about this post