Wani limamin Kiristoci a ƙasar Zimbabwe ya bayyana mafarki na biyu da ya ce ya yi a kan Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa na Najeriya, Bola Tinubu.
“Ubangiji ya ce na yi masa addu’a kan rashin lafiya, kuma zai yi wahala ya kammala wa’adin mulkin sa. Saboda haka ka yi masa addu’a.”
Fasto Passion Java dai ya Sha gargaɗi da barazana daga ‘yan Najeriya, masu cewa kada ya bayyana mafarki na biyu da ya ce ya yi kan Tinubu, amma sai da ya bayyana ɗin.
Ko a mafarkin sa na farko kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, an yi tata-ɓurza da shi.
A ranar Lahadi ɗin nan kuma, Java wanda shi ne babban limamin Cocin Kingdom Embassy, ya ce tuni ya ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya.
Java dai makusancin Shugaban Zimbabwe Emerson Mnangagwa ne, ya yi alƙawarin yi wa Najeriya dirar mikiya cikin 2023.
Duk da dai bai ambaci suna ba, amma ya ce sunan wanda zai lashe zaɓen 2023 na farawa da “T”, wanda hakan kenan za a iya cewa da Tinubu ya ke. Musamman kuma ga shi ya ƙara da cewa, “wanda sunan na sa ke farawa da “T” ya na saka tabarau.
A tattaunawar da aka yi da shi baya-bayan nan, ya ce Ubangiji ya yi masa ilhama cewa ya shaida wa ‘yan cewa abokan adawa za su haɗa hannu da shi.
“Ubangiji ya shaida min cewa abokan adawa za su bi Tinubu, za su yi ƙoƙarin ganin ba a rantsar da shi ba. Amma dai za a rantsar da shi ɗin.
“Amma bayan an rantsar da shi, zai yi masu tayin haɗa kai a bunƙasa Najeriya. Ubangiji ya ce min za su karɓi tayin sa.”
Daga nan ya ce min ya gani a ilhamar da aka yi masa cewa zai yi wahala Tinubu ya kammala wa’adin mulkin sa, saboda rashin lafiya.
“Daga ƙarshe, Ubangiji ya ce a yi wa zaɓaɓɓen shugaban addu’a saboda rashin lafiyar da ke damun sa. Saboda abokan gaba za su ƙalubalanci rashin lafiyar sa, kuma zai yi wahala ya kammala wa’adin
mulkin sa. Saboda haka ya na buƙatar addu’a.”
Tuni dai ‘yan Najeriya ke ta maida wa Fasto Java zafafan raddi.
Discussion about this post