An fallasa yadda tsohon Ministan Makamashi Mohammed Wakil da wasu ‘yan ƙadaba-ƙadaba su ka yi watandar Naira miliyan 450 daga kuɗin cuwa-cuwar zaɓen 2015 a jihar Barno.
An fallasa su ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Maiduguri, a Jihar Barno ranar Talata.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Wakil, sai kuma Garba Abacha, Ibrahim Shehu Birma, Abubakar Ali Kachalla da kuma Muhammad Babba Kachalla tun a cikin 2019.
An zarge su da karɓar Naira miliyan 450 daga ciki dala miliyan 115 wadda tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Diezani Alison-Madukeke ta kamfata ta bayar domin a ci zaɓen 2015 ko ta halin ƙaƙa.
Dukkan waɗanda ake zargin dai sun ƙi yarda da aikata laifin da ake tuhumar su da aikatawa.
A ranar Talace EFCC ta bayar da cikakken bayanin yadda waɗanda ake zargi da aikata ƙaƙudubar su ka yi watandar kuɗaɗen da su ka kamfata.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Talata, ya ce lauyan EFCC Muktar Ahmed ya gabatar da mai shaida na uku, mai suna Dauda Umar.
Mai bayar da shaida ya bayyana wa kotu irin yadda tsohon Minista Wakili ya je har bankin Fedility ya karɓi tsabar kudi har Naira miliyan 450.
Ya ce shi da Garba Abacha su ka je bankin su ka karɓi kuɗin, bayan ya sa hannu kan cakin kuɗin da ya cike kafin a ba shi maƙudan kuɗaɗen.
Mai bayar da shaida ya ci gaba da bayyana yadda aka raba kuɗaɗen a gidan Minista Wakil, a Maiduguri.
Mai Shari’a J.K Dagat ya ɗage shari’ar sai ranar 14 Ga Yuni domin a ci gaba da saurare.