Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci duka bankin kasar nan su ci gaba da ba kwastamomi tsoffin kuɗi sannan su rika amsar su idan aka kawo su ajiya.
Wannan umarni na kunshe a wata takarda wanda babban direkta a bankin Isa Abdulmumini, ya saka wa hannu ya ce daga yau duka bankuna su ci gaba da mu’amula da tsoffin takardun kuɗi.
” A dalilin hukuncin Kotun Koli, babban bankin kasa CBN, ta umarci bankunan Najeriya duka su ci gaba da mu’amala da tsoffin takardun kuɗi na nair 200, 500, 1000 har sai 31 ga Disambar 2023.
Umarnin Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya CBN ba shi da wata dalili ko hujjar da zai sa ya ki bin umarnin kotun Koli kan hukuncin da kotun ta yanke game da ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi.
Kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya sanar da haka a wata takarda da ya saka wa hannu ranar Litinin in da a ciki ya kwarzanta shugaba Buhari a matsayin mutumin da ba ya wasa da duk wani abu da ya shafi dokar kasa da hukuncin kotu.
” Tun da aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a 2015, bai taɓa kin bin umarnin kotu ba ko kuma ya yi wasa da dokokin kasa. Shi mutum ne dake mutanta dokoki da bin su Ka-in-da-na-in.
” Sannan kuma game da tsarin sauya fasalin takardun kuɗin ƙasa da babban bankin kasa yayi, abune da yayi matuƙar tasiri a kasar nan. Eh mutane sun wahala amma kuma abu ne da aka yi domin ci gaban kasa musamman dakile ayyukan ta’addanci da kuma samar da yanayi na yin kasuwanci ba tare da damfara almundahana ba.
” Saboda haka ba a yi wa Buhari adalci ba idan aka ce wai shine ake jira domin abi umarnin kotun koli, Babban Bankin Najeriya CBN ne ke da wannan iko kuma sannan ba hujja baxe kin bin dokar kotun koli da sunan wai tana jiran Buhari ya yi magana.
A karshe Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya yi tir da masu yi masa lakabi da wai shi mutum ne da baya tausayin talaka, yana mai cewa tun da aka kafa kasa Najeriya ba a taba yin shugaba mai tausayin talaka irin Buhari ba. Domin kuwa shine ya kirkiro shirye shirye da tsare-tsaren don taimaka wa talaka a kasar nan da wata gwamnati bata taba yin irin sa ba