Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Mala Buni na Yobe a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Farfesa Umaru Pate jami’in hukumar zabe na INEC ne ya sanar da sakamakon zaben a Damaturu babban birnin jihar a ranar Lahadi.
Pate ya ce Buni na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 317,113 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Sherif Abdullahi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 124, 259.
“Buni Mai Mala na APC bayan ya cika dukkan sharuddan da doka ta gindaya ina bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Yobe.
Pate, kuma mataimakin shugaban jami’ar tarayya Kashere da ke Gombe, ya ce Garba Umar na jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) ya zo na uku da kuri’u 14,246, yayin da Arabi Mohammed na jam’iyyar Action Alliance (AA) ya samu kuri’u 3,260.
Ya ce adadin wadanda suka yi rijistar zabe ya kai 1,485,141, yayin da adadin wadanda aka tantance suka kai 459,492, an kaɗa kuri’u 444,567, 13,214, kuma sun lalace.