Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya aika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika ta musamman yana rokon shugaban kasa da ya gaggauta sa wa a kama dan takarar gwamnan jihar na APC, Sadique Abubakar bisa zargin wai yana kokarin tada hankalin jama’a a jihar.
Gwamna Bala ya ce ” Tunda aka fara kamfen dan takarar APC Sadique Abubakar ya ke yin abin da yaga dama a fadin jihar. Yana yawo da dakaren jami’an tsaro yana tsorata mutanen jihar.
” Sadiq Baba yana tafiya ne da ayarin jami’an tsaro dauke da makamai da ‘yan baranda da aka kawo daga wajen jihar domin ta’addancin ‘yan adawar siyasa da ‘yan jiha da ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 3 da ba su ji ba ba su gani ba tare da jikkata wasu da dama na kananan hukumomin da ya ziyarta.
“Tawagar Sadique na APC sun hada da ‘yan majalisar wakilai biyu Yakubu Dogara da Yakubu Musa Abdullahi, Malam Isah Yuguda, tsohon gwamnan jihar Bauchi, Hon Abdulmumin Kundak, kwamishinan ‘yan sanda, mai ritaya, Bello Illelah, wanda shi ne mai dauka da kula da horas da kwamandojin yakin ci wa mutane mutunci a jihar.
Ina so in sanar maka cewa a matsayin sa na tsohon babban hafsan sojojin saman Najeriya, har yanzu za ka rika ganin sa da zakakumen sojoji da manyan motocin yaki suna raka shi duk inda za shi, yana firgita mana mutane.
A dalilin haka gwamna Bala, ya yi kira ga Buhari ya sa a kama Sadique a tsare shi.