Tsohon kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya ja zugan ƴan APC tare da tawagar ɗan takarar gwamnan jihar Abubakar Sadique, zuwa garin Duguri, garin haihuwar gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed domin yin Kamfen.
Sai dai kuma tun kafin tawagar Dogara wanda ɗan PDP ne amma saboda tsananin gaba da ke tsakanin sa gwamna jihar, ya sa gar-da-gar ya fito karara ranar Alhamis domin yi wa Sadique Kamfen a kada gwamna Bala, suka ci karo da ƴanbPDP da suka datse hana.
Magoya bayan PDP sun datse hanyar shiga garin Duguri, garin gwamna Bala amma da yake tawagar APC na da yawan gaske suka turmushe su suka kutsa cikin garin.
Sai zai kuma ba a nan ne gizo ke sakar ba, domin a daidai ɗan takarar gwamna, Sadique na magana ga dandazon mutane sai suka fara jin ruƙugin tashi harbin bindiga da kusa da wirin taron.
Wani da ya halarci gangamin ya ce tun daga lokacin da mutane suka ji harbin bindigan suka doshi wurin sannan suka kutsa har cikin gidajen dake kusa da wurin suka kamo waɗanda suka riƙa harbin.
Daga nan ne fa aka kaure da rikici da yayi sanadiyyar ran mutum ɗaya sannan wasu mutum shida suka ji rauni, ciki harda jami’an Sibul Difens biyu.
Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da za a buga zaɓe mai zafin gaske ranar 18 ga Maris. Baban dalili kuwa shine ganin yadda ƙarara ƴan jam’iyyar gwamnan da kan sa ke adawa da shi.