An fara shari’ar wata mata mai shekaru 37, wadda ta zargi Gwamna Udom Emmanual na Akwa Ibom cewa ya yi lalata da wata matar aure.
Ana tuhumar matar mai suna Blessing Edit da laifin ɓata sunan Gwmna Udom, bayan ta wallafa zargin kwartanci kan gwamnan a shafin ta na WhatsApp.
An maka ta a gaban Mai Shari’a Ahmed Mohammed na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka tuhume ta da laifuka shida, amma duk ta ce ba ta aikata ba.
Caji na farko da ‘yan sanda su ka gabatar wa kotu shi ne, “Ana zargin Blessing Ossom mai shekaru 37 da ke zaune a gida mai lamba 18, Buchanan Cresent, Wuse II, Abuja da laifin wallafa “sunayen Matan Aure ‘Yan Siyasar da Gwamna Emmanual ke wa kwartanci na tafe, ku saurari jiran sunayen su.”
Mai gabatar da ƙara ya ce Blessing ta yi waccan rubutun ɓatanci a shafin ta na Facebook.
Sannan kuma ana tuhumar ta da wallafa wani saƙon, “Jama’a za mu fara fallasa fallasassu. Ku jira ku sha mamaki.” Ta yi haka ne duk a shafin ta na Facebook.
Wani zargin da ake mata kuma shi ne, ta buga labarin cewa, “Yanzu Gwamnan Akwa Ibom da Kwamishinar Harkokin Mata ya ke kwana. Ita ce farkar sa, ta ƙwace wa Uwargidan Gwamna miji.”
Mai gabatar da ƙara ya ce rubuce-rubucen da Blessing ta yi ya karya dokar Sashe na 24 na laifin ‘yan soshiyal midiya, doka ta 2015.
Sai dai Mai Shari’a ya bayar da belin ta kan kuɗi Naira 500,000, tare da mai karɓar beli, wanda zai kasance ma’aikacin gwamnati ne, kuma mai rufin asiri.
Daga nan ya umarci Blesssing ta bai wa kotu fasfo ɗin ta na fita waje. Kuma idan ta kasa cika sharuɗɗan beli, to a tasa ƙeyar ta zuwa kurkukun Suleja.
Mai Shari’a ya ce za a ci gaba da shari’ar a ranar 10 Ga Mayu.