Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa tunda yake bai taba ganin jagwalgwalallen zaɓe ba kamar wanda aka yi a karshen makon jiya.
Atiku ne ya zo na biyu a sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayyana ranar Talata a Abuja.
Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen da kuri’u sama da Miliyan 1.
Sai dai tun bayan sanar da sakamakon zaɓen Ariku da Peter Obi suka kalubalanci sakamakon zaɓen inda suka yi kira ga Hukumar zabe ta soke zaɓen kwatakwata a sake shi daga farko.
Yanzu dai abin gaba daya ya zama kamar wasan yara. Duka manyan jam’iyyun hudu kowannen su ya ce shine yayi nasara a zaɓen.
A taron manema labarai da Atiku yayi ranar Alhamis, ya ce an yi masa fashin nasarar da ya samu ne a zaɓen shugaban kasa.
” Tun da Najeriya ta dawo mulkin dimokuraɗiyya a 1999, ban taɓa ganin shiriritar zaɓe irin wannan ba. Wannan zaɓe cike yake da jagwalgwalo da kamayamaya daban-daban da ni dai ban taba ganin irin sa ba.
” Saboda haka ba zan yarda ba da sakamakon da hukumar zaɓe ta yi gaggawar faɗi ba saboda ta san babu gaskiya a cikin sa. Saboda haka zan garzaya kotu domin ya kwato min hakki na.
A karshe bayan tada jijiyoyin wuya da murza gashin baki da ya yi a gaban jigajigan PDP da suka raka shi da manema labarai, ya ce kowa ya zauna lafiya, zai bi hakkin sa a kotu.